Jami’an tsaro a Jamhuriyar Nijar sun yi nasarar cafke ƙasurgumin ɗan bindigar nan Ɓaleri, wanda ake nema ruwa a jallo a Najeriya.
Alfijir labarai ta dakarun runduna ta musamman da ake yi wa laƙabi da Farautar Bushiya (Faraoutar Bushiya), sun kama shi ne a garin Rigar Kowa Gwani, da ke yankin Gidan Rumji a jihar Maraɗi.
A sanarwar da hukumomin sojin Nijar suka bayar, sun ce an damƙe Ɓaleri ne da misalin ƙarfe 1 na rana a lokacin ya yake wata ganawa da yaransa kan yadda za su kai hari Najeriya da Nijar.
Rahotanni sun ce Ɓaleri wanda ɗan asalin Shinkafi ne a jihar Zamfara, wanda ya tsere daga Najeriya , ya jima yana addabar jama’a a yankunan jihar ta Zamfara da kuma Maraɗi a Nijar.
Kuma makusanci ne ga ƙasurgumin ɗanbindigar nan da shi ma ya yi ƙaurin suna a arewacin Najeriya, Bello Turji.
Ɓaleri shi ne na 40 a jerin mutanen da hukumomin sojin Najeriya suka fi nema ruwa a jallo, inda aka sanya lada na musamman ga duk wanda ya kama shi ko ya bayar da labarin inda za a same shi.
BBC Hausa
Domin Samun sauran shirye shiryenmu sai nemesis a 👇
https://twitter.com/Musabestseller?s=09
https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165
https://www.threads.net/@alfijirlabarai
https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12
https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag
Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇👇
https://chat.whatsapp.com/ELQRQyq1zGn7zpAVP8DwNj