Hukumar da ke yaki da masu yi wa tattalin arzikin kasa zagon kasa (EFCC) ta fara gudanar da bincike a kan zargin karkatar da wasu Kudade na yakin neman zaben jam’iyyar NNPP na zaben 2023 da kuma gazawar kwamitin amintattu na kasa da Kwankwaso ya jagoranta wajen biyan wakilan jam’iyyar da suka yi wa jam’iyyar aiki a zaben shugaban kasa da na gwamnoni a 2023, a fadin kasar nan.
Alfijir labarai ta ruwaito rahotanni sun nuna cewa hukumar EFCC ta gayyaci sakataren jam’iyyar na kasa, Kwamared Oginni Olaposi Sunday don tabbatar da zarge-zargen da ake yi wa Sanata Kwankwaso da sakatariyar sa mai zaman kanta, Misis Folashade Aliu, wanda ake kyautata zaton Kwankwaso ya yi amfani da ita wajen karkatar da kudaden jam’iyyar da asusun yakin neman zabe ya samu ta hanyar karo-karo.
Sai dai karar da Oginni ya shigar ta kuma tuhumi wadanda suka rattaba hannu a asusun jam’iyyar na bankin UBA wadanda suka hada da Farfesa Rufa’i Alkali da Abba Kawu da Dipo Olayokun.
“Saboda haka, hukumar ta EFCC ka iya bincikar yadda aka Dipo Olayokun ya tara dukiyarsa cikin kankanin lokaci da kuma yadda ya mallaki kadarori a yankunan da ke Abuja cikin kasa da shekaru biyu na mulkin sa a matsayin wanda ya ke sanya hannu a asusun NNPP.
Da yake tabbatar da faruwar lamarin a wani jawabi da ya yiwa jaridar Vanguard ta wayar tarho a Abeokuta, sakataren jam’iyyar na kasa, Kwamared Oginni ya ce, ya amsa gayyatar da EFCC ta yi masa zuwa hedikwatar hukumar da ke Abuja a ranar Larabar da ta gabata.
Ya kara da cewar ya yi bayani da karin haske kan karar da ya sanya wa hannu a madadin jam’iyyar, inda suke zargi Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso da tawagarsa da almundahanar Naira biliyan 2.5.
“Hakika EFCC ce ta gayyace ni. Na kuma girmama wannan gayyata kuma na gamsu da kwarewar jami’an EFCC. Na amsa tambayoyin da suka shafi takardar koke da na sanya wa hannu a madadin NNPP ba tare da tsangwama ba.
Dangane da gayyatar da EFCC ta yiwa sakataren jam’iyyar NNPP na kasa, ta bayyana a fili cewa an fara bincike kan karar da aka shigar ana zargin Sanata Kwankwaso da almundahanar kudaden jam’iyyar NNPP.
SOLACEBASE
Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a
https://twitter.com/Musabestseller?s=09
https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165
https://www.threads.net/@alfijirlabarai
https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12
https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag
Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇👇
https://chat.whatsapp.com/ELQRQyq1zGn7zpAVP8DwNj.