Fadar shugaban kasa ta musanta zargin da jagoran jam’iyyar NNPP na kasa, Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso ya yi na cewa gwamnatin tarayya na shirin kafa dokar ta baci a jihar Kano.
Kwankwaso ya yi zargin jam’iyyar APC a karkashin gwamnatin tarayya ta dauki bangare a rikicin Sarautar Kano.
Fadar shugaban kasar tace ba wani shiri na sanya dokar ta baci don kawar da gwamnati dimokuradiyya a wata jiha, inda ta ce “jita-jita ce kawai yake yadawa da rudani.
Mai magana da yawun shugaban kasa, Bayo Onanuga, ya shaidawa jaridar The Nation a daren Litinin cewa, babu wani yanayi da zai sa a sanya dokar ta baci a jihar.
Sai dai fadar shugaban kasar ta ce: “Babu gaskiya a ciki. Jita-jita ce kawai. Gwamnatin Tarayya ba za ta iya kafa dokar ta-baci a kowace jiha ba tare da sa hannun Majalisar Tarayya ba. Babu wannan batu wannan batu Jita-jita ce kawai.
“Majalisar dokokin kasa tana hutu. Babu wani shugaban da zai iya tashi kawai ya ayyana dokar ta-baci a kowace jiha.”
Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a
https://twitter.com/Musabestseller?s=09
https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165
https://www.threads.net/@alfijirlabarai
https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12
https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag
Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇👇
https://chat.whatsapp.com/ELQRQyq1zGn7zpAVP8DwNj