Gwamnatin Jihar Jigawa tace ta kwace dazukan gwamnati a hannun jama’a, za kuma a bada aron su ga jama’a domin yin noma.
Alfijir labarai ta ruwaito Gwamna Umar Namadi ya bayyana hakan a lokacin hawan bariki da mai martaba sarkin Dutse ya kai masa a gidan Gwamnati.
Malam Umar Namadi, yace Gwamnatin jihar ta kwace duk wani daji da makiyayu da burtalai da aka bayar ba bisa ka’ida ba, tare da haramta yin noma a cikin su.
Yana mai cewa an kafa kwamiti domin duba wannan lamari kuma tuni kwamitin ya bada rahotan wucin gadi.
Ya ce shugabannin kananan hukumomi da Hakimai da Dagatai da masu unguwanni su ne babbar matsalar dake tattare da matsalar dazuka a jihar Jigawa.
A don haka, Namadi ya yi gargadin cewa duk shugaban karamar hukuma ko Hakimi ko Dagaci ko mai unguwa da aka samu ya bada daji ba bisa ka’ida ba zai fuskanci fushin hukuma.
Yayi nuni da cewar gwamnati zata kai doka majalissar dokokin jihar domin hana sarar itatuwa a fadin jihar jigawa.
Da ya waiwayi batun takin zamani kuwa, Gwamnan ya ce Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya bada takin zamani tirela 80 domin rabawa al’ummar jihar Jigawa kyauta.
Kazalika, ya ce itama gwamnatin jihar ta siyo takin domin sayarwa manoma a farashi mai sauki.
Gwamna Namadi ya ce an kafa kwamiti domin sa ido wajen rabon takin zamanin na shugaban kasa da kuma wanda gwamnatinsa za ta sayarwa manoma.
Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a
https://twitter.com/Musabestseller?s=09
https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165
https://www.threads.net/@alfijirlabarai
https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12
https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag
Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇👇
https://chat.whatsapp.com/ELQRQyq1zGn7zpAVP8DwNj