Gwamnan Kano ya sake kaddamar da biyan yan fansho Naira miliyan dubu biyar a Karo na biyu.

FB IMG 1719763546663

Da yake jawabi yayin kaddamar da biyan kudin, gwamna Abba Kabir Yusuf ya ce fansho dubu hudu ne zasu amfana daga kudaden da aka ware.

Alfijir labarai ta ruwaito Gwamna Abba Kabir Yusuf yace a wannan Karo, manyan ma’aikatan gwamnati zasu amfana da kaso sittin na kudaden da aka ware yayin da kananan ma’aikata zasu amfana da kaso arbin.

Kazalika gwamna Abba Kabir Yusuf yace yan fanshon da kudinsu ya kama daga Naira miliyan daya zuwa naira miliyan biyar zasu amfana kama daga ma’aikatan gwamnatin jiha dana kananan hukumomi.

Ya jaddada cewa, gwamnati ta kafa kwamitin amintattu wanda zai sanya idanu domin tabbatar da an raba kudin yadda ya kamata.

Ya yi alwashin gwamnatinsa zata cigaba da biyan yan fansho hakkokinsu har sai ta kammala biyan kudi Naira biliyan 45 da yan fanshon jihar Kano suke bin gwamnatin jiha.

Daga nan ya bukaci kungiyar yan fansho su bi hanyar Sharia domin neman hakkokinsu, kasancewar babu sisin kwabo daga cikin kudin da suka yanka da ya shiga asusun gwamnatin jiha.

Ya bayyana godiyarsa ga kungiyar yan pansho ta kasa bisa karramashi da tayi a matsayin gwamnan da yafi dukkanin gwamnonin kasar nan kula da Yan fansho da biyansu hakkokinsu.

A nasa bangaren, shugaban kungiyar yan fansho na jiha, Comred Salisu Ahmad Gwale, ya godewa gwamna Abba Kabir Yusuf bisa cusa  farin ciki a zukatan Yan fansho, kasancewar babu wani gwamna da ya ware kudaden da gwamnatinsa ta ware a fadin jihar Kano.

Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

https://www.threads.net/@alfijirlabarai

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇👇

https://chat.whatsapp.com/ELQRQyq1zGn7zpAVP8DwNj

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *