A wani gagarumin aikin jin kai, shugaban gamayyar jami’o’in MAAUN, Farfesa Adamu Abubakar Gwarzo, ya bayar da gudunmuwar naira miliyan 5 dom…
Alfijir labarai ta ruwaito a wani gagarumin aikin jin kai, shugaban gamayyar jami’o’in MAAUN, Farfesa Adamu Abubakar Gwarzo, ya bayar da gudunmuwar naira miliyan 5 domin tallafa wa ilimin marayu 30 da suka yi rijista a matakin firamare a makarantan Intercontinental Kano.
Farfesa Gwarzo ya sanar da bayar da gudunmawar ne a lokacin bikin bayar da lambar yabo ta makarantar na shekarar 2023/2024 a taron ilimi da aka gudanar a dakin taro na ‘Afficient Event Centre’ dake Kano a ranar Talata.
A cewar sa, wannan karamcin zai taimaka matuka wajen tallafa wa daliban su ci gaba da karatunsu na sakandare bayan kammala karatunsu na firamare a makarantar.
Wannan gagarumar gudunmawar an bayar da ita ne da nufin bunkasa damar ilimi ga waɗannan yara, tare da tabbatar da cewa sun sami abubuwan da ake da bukata na tallafi domin bunƙasa iliminsu.
Kazalika, Farfesa Gwarzo ya kuma bayar da gudunmuwar Naira miliyan 2.5 ga daliban da suka fi kowa kwazo da aka yaye a matakin firamare da sakandire ciki har da dalibai biyu na sakandire ‘yan aji uku da suka fi kowa kokari inda kowannensu ya tafi gida da Naira 500,000.
A jawabinsa Farfesa Gwarzo ya tunatar da iyaye kan bukatar da yake akwai na maida hankali kan karatun sakandire bisa la’akari da muhimmancinsa.
Ya kuma jaddada wajibcin da ya hau kan iyaye da su saka hannun jari sosai a fannin karatun sakandare na ‘ya’yansu.
Ya yi nuni da cewa makarantar sakandire ita ce ginshiki ce mai muhimmanci da ke tanadin dalibai masu kwazo domin dora karatunsu a matakin jami’a.
Farfesa Gwarzo, wanda ya bayyana shirin kafa jami’a a birnin Paris, ya bukaci wadanda suka mallaki kwalejin da su kafa makarantar sakandare mai harsuna biyu domin baiwa dalibai damar zama masu harshe biyu.
Tun da farko a jawabansu na daban daban, wadanda suka assasa Makarantun, Injiniya Yusuf Baba da Hajiya Hadiza Nuhu Yusuf Baba sun yabawa Farfesa Adamu Abubakar Gwarzo bisa irin gudunmawar da ya bayar a fannin ilimi musamman na kafa jami’a mai zaman kanta mafi inganci a Kano.
Har ila yau, sun nuna matukar godiya ga Farfesa Adamu Abubakar Gwarzo bisa yadda yake ci gaba da tallafa wa makarantar Intercontinental tare da nuna jajircewarsa na ci gaban ilimi ba kawai a Nijeriya ba, har ma a fadin nahiyar Afirka baki daya.
Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a
https://twitter.com/Musabestseller?s=09
https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165
https://www.threads.net/@alfijirlabarai
https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12
https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag
Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇👇
https://chat.whatsapp.com/ELQRQyq1zGn7zpAVP8DwNj