Manjo Al-Mustapha Ya Magantu Akan Masu Kiraye-kirayen Sojoji suyi Juyin Mulki A Najeriya

FB IMG 1723048100390

Manjo Hamza Al-Mustapha, tsohon babban jami’in tsaro na marigayi Janar Sani Abacha, ya yi Allah-wadai da kiraye-kirayen da ake yi na sojoji su karbe iko da Najeriya, yana mai bayyana hakan a matsayin kuskure Kuma bai dace ba. Ya kuma kara da cewa, Babu wani dalili na tsoma bakin sojoji a harkokin siyasar Najeriya, Yana mai jaddada cewa dimokradiyya ta samu gindin zama a kasar.

Alfijir labarai ta ruwaito da yake jawabi a Abuja a yau Laraba, Al-Mustapha ya bukaci masu ra’ayin juyin mulki da su mayar da hankali wajen karfafa biyayyar da sojoji suke yi ga tsarin dimokuradiyya. Ya jaddada cewa mulkin soja ba shi da amfani a yanayin duniya a yau.

Al-Mustapha, wanda a yanzu ya bayyana a matsayin dan siyasa, ya bayyana kudirinsa na ciyar da dimokuradiyya gaba a Najeriya. “Mayar da hankalinmu shine saka hannun jari a cikin kyakkyawan tsarin dimokradiyya. Halin da ake ciki a duniya ya shafi biyayyar soja ga dimokradiyya, kuma ya kamata mu rungumi wannan alkibla yayin da muke ci gaba,” in ji shi.

Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

https://www.threads.net/@alfijirlabarai

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇👇

https://chat.whatsapp.com/ELQRQyq1zGn7zpAVP8DwNj

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *