Gwamnan jihar Bauchi, Sanata Bala Mohammed ya ce yana da kyau gwamnatin tarayyata ta fahimci cewa shirye-shirye ko ƙudurorin da take ɓullo da su ba sa aiki.
Alfijir labarai ta ruwaito yayin da yake jawabi a lokacin ƙaddamar da yaƙin neman zaɓen jam’iyyar PDP a zaɓen ƙananan hukumomin jihar, Gwamna Bala ya ce ya kamata gwamnatin tarayya ta daina fakewa da bai wa ‘yan Najeriya uzuri.
“Manufofin gwamnatin tarayya ba sa aiki. Ya kamata su fahimta cewa matsalarsu da shirye-shiryensu ne ke haddasa matsalolin da ake ciki a ƙasar nan, don haka ya kamata su canja.”
Gwamnan ya kuma ce jawabin da shugaban ƙasar ya yi a ƙarshen makon da ya gabata, fankon jawabi ne da babu wani abin ɗauka a cikinsa.
A ranar Lahadi ne dai shugaba Tinubu ya yi wa al’ummar ƙasar jawabi, inda a ciki ya yi kira ga masu zanga-zangar tsadar rayuwa a ƙasar su jingine ƙudurin nasu tare da rungumar hanyoyin tattaunawa.
To sai dai gwamnan na Bauchi ya ce ”Na saurari duka jawabin shugaban ƙasar cikin nutsuwa da kunnen basira, amma babu komai a cikin a jawabin nasa,”.
“Bai amince da yanayin da ake ciki ba, bai magance abubuwan da suka haifar da matsalolin ba. Matsalolin ba nasa ba ne shi kaɗai, namu ne duka shugabanni kama daga fadar shugaban ƙasar zuwa jihohi da ƙananan hukumomi”.
BBC
Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a
https://twitter.com/Musabestseller?s=09
https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165
https://www.threads.net/@alfijirlabarai
https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12
https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag
Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇👇
https://chat.whatsapp.com/ELQRQyq1zGn7zpAVP8DwNj