Labari Mai Dadi! B U K Ta Amince Da Nada Mal Umar Sani Fagge Da Mai Bushira Da Wasu Malamai A Matsayin Farfesa

Farfesa Umar Sani Fagge

Hukumar gudanarwa ta Jami’ar Bayero (BUK) ta amince da karin girma ga manyan malamai casa’in zuwa matakin Farfesa da Mataimakin Farfesa.

Alfijir Labarai ta rawaito wasu daga cikin wadanda aka yi wa karin girma akwai fitaccen malamin addinin Musulunci, Dokta Umar Sani Fagge, wanda a yanzu ya zama Farfesa a harshen Larabci.

Sai kuma Matabuli Shehu Kabara, dan Sheikh Nasiru Kabara, wanda a yanzu Farfesa ne a fannin Larabci.

Sai Dr. Ibrahim Mu’azzam Saminu Maibushira da Dr. Tijjani Muhammad Na’iya, wanda ya zama Farfesa a tarihin zamantakewa da siyasa.

Alfijir Labarai na taya manyan malamanmu murnar wannan natsayi, Allah ya sanya albarka cikinsa ameen.

Domin samun sauran shirye shiryenmu zaku iya biyo mu ta wannan shafukan👇

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

https://www.threads.net/@alfijirlabarai

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇👇

https://chat.whatsapp.com/ELQRQyq1zGn7zpAVP8DwNj

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *