YANZU YANZU: Gwamna Yusuf Ya Sauke Kantomomin Riƙo Na Ƙananan Hukumomi

IMG 20240918 WA0971

Daga Aminu Bala Madobi

Gwamnan Kano Abba Kabir Yusuf ya sauke dukkanin shugabanin riko na kananan hukumomin jihar 44 nan take.

Alfijir Labarai ta rawaito cikin wata sanarwa Gwamnan ya bada umarnin ne yayin wata liyafa ta musamman da ya yi da shugabannin riko na kananan hukumomi a gidan gwamnati.

Ya umarci shugabannin rikon da su mika jagorancin kananan hukumomin zuwa daraktocin mulki na kowace karamar hukuma wato DPM.

Ya Kara da cewa, umarnin saukewar ya hada da mataimakan shugabanni da sakatarori da kansiloli na kowace karamar hukuma.

Daganan Gwamna Yusuf Ya gode musu bisa kokari da gudummawar da suka bayar wajen cigaban yankunansu tare da jaddada cewa gwamnati zata ci gaba da tafiya dasu a guraben da suka dace.

A jawaban da suka gabatar Shugabannin rikon da wa’adin mulkin nasu yakawo karshe sun godewa gwamna Abba Kabir Yusuf bisa damar da ya basu na hidimtawa al’umarsu tsawon wannan lokacin.

Domin samun sauran shirye shiryenmu zaku iya biyo mu ta wannan shafukan👇

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

https://www.threads.net/@alfijirlabarai

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇👇

https://chat.whatsapp.com/ELQRQyq1zGn7zpAVP8DwNj

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *