Ba Fa Rabon Tallafi Shine Mafita Ga “Yan Najeriya Ba – In Ji Abdulsalami Abubakar

Abdussalam Tinubu

Daga Aminu Bala Madobi

Tsohon Shugaban Kasa  ya roki gwamnatin Tinubu da ta magance tsananin wahalhalu da ake ciki a kasar

Alfijr Labarai ta Abdulsalami ya shawarci gwamnatin tarayya karkashin shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu da ta tunkari mawuyacin hali da ‘yan kasa ke ciki.

Abdussalam ya bayyana hakane jawabi ne a Minna, lokacin da ya karbi bakuncin wata tawaga ta Campaign for Democracy (CD), kungiyoyin fararen hula (CSO).

Yace yanayin halin kunci da ake ciki na neman wuce gona da iri, ya kamata gwamnati ta samar da matakan da za a magance wahalhalun da ‘yan kasar ke ciki a halin yanzu.

“Kowa yana kuka saboda wannan wahalhalun da ake fama da shi, kuma da alama lamarin na neman wuce gona da iri”.

“Mutane ba za su iya cin abinci sau uku ba, batun sufuri, hauhawar farashin man fetur, karin kudin makaranta ga yara da kuma rashin kudi a aljihun kowa yana sabbaba wahalhalu.

“Za mu ci gaba da karfafa gwiwar gwamnati ta bullo da matakan sassauta wannan wahalhalu. Ya kamata gwamnatocin tarayya, jihohi da kananan hukumomi su duba yadda za su shawo kan matsalar tattalin arziki.”

Ya ce a irin wannan yanayi bada kayan agaji ba shi ne mafita ga alumma ba, domin tsadar kayan abinci da sauran kayayyaki a fadin kasar nan abune da ya taazzara.

“Amsar ita ce bukatar gwamnati ta wadata ko ina da kayan more rayuwa, ta sassauto abubuwa domin yan kasa su sami walwala tare da wadatar da al’umma da abinci.

A bar gwamnati ta sayi abinci ta sayar da shi a kan farashi mai rahusa, ta yadda mutane za su iya siyan kayan abincin da suke so, gwargwadon kudin da suke samu,” in ji shi.

Ya shawarci masu shirin yin zanga-zangar adawa da matsalar tattalin arziki a ranar 1 ga Oktoba da su yi hakan cikin lumana.

“Don girman Allah idan kun tashi yin zanga zangar, ku yi shi cikin lumana,” in ji shi.

Tun da farko, shugaban tawagar ya ce sun je gidan tsohon shugaban kasar ne domin taya shi murnar zagayowar ranar haihuwar sa. Sun yi masa addu’ar Allah ya ba shi lafiya da nisan kwana.

Jabi ya nemi goyon bayan tsohon shugaban na Najeriya domin aiwatar da wasu shirye-shiryensa, musamman a fannin zaburar da ‘yan Najeriya domin su samu damar gudanar da mulki.

Ya ja hankalin gwamnati da tayi gaggawar maagance tsananin yunwar da ta addabi ‘yan kasar, ya kuma bukace shi da ya taimaka wajen ganin an shawo kan gwamnatin tarayya don magance matsalar.

Domin samun sauran shirye shiryenmu zaku iya biyo mu ta wannan shafukan👇

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

https://www.threads.net/@alfijirlabarai

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇👇

https://chat.whatsapp.com/ELQRQyq1zGn7zpAVP8DwNj

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *