Wasu ‘yan bindiga dauke da muggan makamai sun kai farmaki garin Dan-Ali da ke karamar hukumar Danmusa a jihar Katsina, inda suka dakile sallar Juma’a a masallatai da dama.
Alfijir labarai ta rawaito maharan dauke da makamai sun kutsa kai cikin yankunan, inda suka rika harbe-harbe, lamarin da ya haifar da firgici tare da tilasta wa masu ibada gudu.
Wata majiya daga cikin al’ummar ta tabbatar da faruwar lamarin.
Ya ci gaba da cewa, “Muna cikin Sallar Juma’a ne muka ji harbin, sai kowa ya ruga da gudu. Ba mu iya sake yin addu’o’inmu ba. Godiya ga jami’an tsaro da ke yankin da suka yi musu zazzafar kora.”
Domin samun sauran shirye shiryenmu zaku iya biyo mu ta wannan shafukan👇
Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇👇