Gwamnan Kano ya aikewa tsofaffin kansilolin jihar sako akan hakkinsu

FB IMG 1715254046724

Gwamnan Jihar Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf, ya sake jaddada kudirin gwamnatinsa na biyan ragowar haƙƙoƙin tsoffin kansiloli, wanda wasu daga ciki ke nan tun daga shekarar 2014.

Alfijir labarai ta rawaito wannan tabbacin ya fito ne cikin wata sanarwa da kakakin gwamnan, Sunusi Bature Dawakin Tofa, ya fitar a ranar Talata.

Sanarwar ta fito ne a yayin wani taro da aka gudanar, inda tsoffin kansiloli daga jam’iyyar APC suka shiga jam’iyyar NNPP ta hannun kungiyar Maslaha Forum na kansiloli, masu lura da ayyuka, da masu ba da shawara na jihar Kano.

Gwamna Yusuf ya jinjinawa kansilolin bisa ga shawarar da suka yanke na sauya sheka, inda ya danganta matakin nasu da rashin gamsuwa da gwamnatin baya wajen biyan haƙƙoƙinsu.

“Shawarar su ta yi dai-dai,” in ji Yusuf, “kuma ina tabbatar musu cewa za a biya su haƙƙoƙinsu nan ba da jimawa ba.”

Ya bayyana cewa an kafa wani kwamitin da zai jagoranci tsarin biyan kudaden, wanda zai bi tsari irin na masu karɓar fansho.

Haka kuma, ya umurci sabbin shugabannin ƙananan hukumomin Kano guda 44 su gano dukkan tsoffin kansilolin da ba a biya haƙƙoƙinsu ba tukuna.

Domin samun sauran shirye-shiryen Alfijir labarai/Alfijir news zaku iya bibbiyarmu ta 👇

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

https://www.threads.net/@alfijirlabarai

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

Alfijir labarai Alfijir News Whatsapp Group 👇👇

https://chat.whatsapp.com/ELQRQyq1zGn7zpAVP8DwNj

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *