Ana Wata! Tsohon shugaban NNPP kuma tsohon shugaban Gidan Radiyo Kano ya fice daga jam’iyyar

NNPP

Tsohon shugaban jam’iyyar NNPP a Kano kuma tsohon shugaban Gidan Rediyon Kano, Hisham Habib ya fice daga jam’iyyar zuwa jam’iyyar adawa ta APC a jihar.

Alfijir labarai ta rawaito Hisham ya baiyana cewa ya fice daga jam’iyyar NNPP ne saboda “abubuwa ba sa tafiya yadda ya kamata”.

Ya shaidawa manema labarai cewa ya fice daga NNPP zuwa APC ne bayan tuntuba da ya dauki lokaci yana yi, inda daga bisani ya yanke shawarar ficewa.

Ya kuma godewa Gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf bisa damar da ya bashi ya hidimtawa Kano na dan wani lokaci.

Domin samun sauran shirye-shiryen Alfijir labarai/Alfijir news zaku iya bibbiyarmu ta 👇

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

https://www.threads.net/@alfijirlabarai

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

Alfijir labarai Alfijir News Whatsapp Group 👇👇

https://chat.whatsapp.com/ELQRQyq1zGn7zpAVP8DwNj

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *