Shugaban Najeriya Bola Tinubu yai naɗa sabbin muƙamai guda huɗu

FB IMG 1723115651747

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya amince da naɗin Daniel Bwala a matsayin mashawarcinsa na musamman kan harkokin yaɗa labarai.

Alfijir labarai ta rawaito mai magana da yawun shugaban ƙasar Bayo Onanuga ne ya bayyana hakan cikin wata sanarwa da ya fitar a yammacin ranar Alhamis.

Daniel Bwala dai tsohon hadimi ne ga tsohon Mataimakin Shugaban Najeriya, Atiku Abubakar.

Onanuga ya kuma sanar da naɗin wasu sabbin muƙamai da Shugaba Tinubu ya tabbatar da suka haɗa da Mista Olawale Olapade a matsayin Darekta-Janar na Hukumar Wasanni da Dokta Abisoye Fagade a matsayin Darekta-Janar na Hukumar Karɓar Baƙi da Yawon Buɗe Ido.

Haka kuma, hadimin shugaban ƙasar ya sanar da naɗin Dokta Adebowale Adedokun a matsayin Darekta-Janar na Hukumar Da ke sa ido kan saye-sayen Gwamnati.

Domin samun sauran shirye-shiryen Alfijir labarai/Alfijir news zaku iya bibbiyarmu ta 👇

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

https://www.threads.net/@alfijirlabarai

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

Alfijir labarai Alfijir News Whatsapp Group 👇👇

https://chat.whatsapp.com/ELQRQyq1zGn7zpAVP8DwNj

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *