Mun kwato kadarori da kudade na kimanin Naira biliyan 105.8 cikin shekara daya – Cewar ICPC

ICPC Chairman

Musa Aliyu, shugaban Hukumar Yaki da Cin Hanci da Rashawa (ICPC), ya ce hukumar ta kwato kadarori da kudade da darajarsu ta kai Naira biliyan N105.82 tsakanin shekarar 2023 da 2024.

Alfijir labarai ta rawaito cikin wata sanarwa da Demola Bakare, mai magana da yawun ICPC, ya fitar, an bayyana cewa Aliyu ya yi wannan jawabi ne a ranar Laraba yayin ziyarar ‘yan kwamitin majalisar wakilai kan yaki da cin hanci.

“Hukumar ta karɓi ƙorafe-ƙorafe 1,187 a shekarar 2023. Daga Janairu zuwa Oktoba 2024, hukumar ta karɓi ƙorafe-ƙorafe 851. A shekarar 2023, ta samu hukuncin kotu 18, yayin da a shekarar 2024 ta samu hukuncin kotu 13,” in ji Bakare, yana ambaton Aliyu.

“Kadarori da kudaden da aka kwato sun kai Naira biliyan 76.75 a shekarar 2023, yayin da a shekarar 2024, ICPC ta kwato Naira biliyan 29.07.”

Aliyu ya ce hukumar tana yin aiki tare da muhimman abokan hulɗa da sauran hukumomin da suka dace domin yaki da cin hanci da rashawa.

Domin samun sauran shirye-shiryen Alfijir labarai/Alfijir news zaku iya bibbiyarmu ta 👇

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

https://www.threads.net/@alfijirlabarai

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

Alfijir labarai Alfijir News Whatsapp Group 👇👇

https://chat.whatsapp.com/ELQRQyq1zGn7zpAVP8DwNj

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *