Daga Muhd Sanusi Uba
Sarkin Beli Muhammad Inuwa, an haifeshi a shekara ta 1908, an kuma naɗa shi Sarautar a shekara ta 1933 a matsayin Sarkin Beli dake ƙaramar Hukumar Shira jihar Bauchin Yakubu.
Yayi zamani da sarkin katagum Abdulƙadir 1933 wanda yayi shekara 12 karkashin mulkinsa
Sannan kuma yayi zamani da Marigayi sarkin katagum Umaru farouk I wanda yayi shekara 35 yana sarauta.
Sannan kuma Yayi zamani da Sarkin katagum Muhammad kabir Umar wanda yayi shekara 37 yana sarauta.
Sannan Yayi zamani da Sarkin katagum na yanzu Mai martaba sarki Umaru farouk II shekara 6 yanzu.
A Kanon Dabo kuwa Yayi zamani da sarakuna 6.
Yayi zamani da Sarkin kano Abdullahi bayero wanda ya shekara 20 yana sarauta.
Sannan Yayi zamani da sarkin Kano Muhammad sunusi na I Shekara 9 yana sarauta.
Sannan Yayi zamani da Sarkin kano Muhammad Inuwa wanda tayi wata 4 bisa karaga.
Sannan Yayi zamani da Sarkin kano Ado bayero wanda ya share shekaru 52 yana sarautar Kano.
Sannan Yayi zamani da sarkin Kano Sunusi II wanda yayi shekara 6 yana sarauta.
Sai sarkin Kano na yanzu Aminu Ado bayero Shekara 3.
A Katsina kuwa Yayi zamani da sarakuna 4.
Yayi zamani da Sarkin Katsina Muhammadu Dikko wanda yayi shekara 38 yana sarauta.
Sannan Yayi zamani da Sarkin Katsina Sir Usman Nagogo wanda ya shekara 37 yana sarauta.
Sannan Yayi zamani da Sarkin Katsina Muhammadu Kabir Usman 26 yana sarauta.
Sai yanzu yana zamani da Sarkin Katsina Abdulmuminu Kabir Usman wanda ya keda shekaru 15 bisa karagar mulkin Katsina.
Kuma har yanzu sarkin Beli yana nan da ransa da kuma Lafiya.
A kwanakin baya bayan nan, an samu labarin mutuwar sarauniyar England Queen Elizabeth da ta kai shekaru 70 bisa gadon sarauta, mutane da yawa suna ganin sarauniyar ta daɗe bisa mulki.
Idan aka lissafa tana shan jinjirarta sarkin Beli ya fara sarauta, domin shekarunta 92 ta mutu shi kuma shekararsa 90 yana mulki.
Bama tsammanin akwai wani sarki a ƙasar Hausa daya taɓa Haura irin wayann shekarun yana sarauta.
Allah ya jikansa da gafara Allah ya bawa iyalansa da sauran masoya hakurin rashinsa.
Wannan tarihin an yi shine shekara biyu da suka wuce ba a yau aka yi ba, duba da wasu na tunanin Muna da wani bangare a masarautar Kano! Jaridar Alfijir ta kowa ce bata bangarenci a aikinta.
Don haka mabiyanmu sai dai kuyi hakuri wani lokacin zaku ji dadin labaranmu wani lokacin su zo muku akasin haka, yanayin aiki ne.
Domin samun sauran shirye-shiryen Alfijir labarai/Alfijir news zaku iya bibbiyarmu ta 👇
https://twitter.com/Musabestseller?s=09
https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165
https://www.threads.net/@alfijirlabarai
https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12
https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag
Alfijir labarai Alfijir News Whatsapp Group 👇👇
https://chat.whatsapp.com/ELQRQyq1zGn7zpAVP8DwNj