Hukumar DSS Da EFCC Zasu Lashe Man Fetur na Biliyan 2 a Motocin su a 2025

FB IMG 1735991632008

Daga Aminu Bala Madobi

Hukumar tsaron farin kaya DSS Da Kuma EFCC za su kashe naira biliyan biyu wajen zuba man fetur ga motocinsu a shekara ta 2025.

Cikin wani rahoto da jaridar Punch ta gani a cikin daftarin kudurin kasafin kudi, ta hango inda aka warewa hukumomin Kudaden daza suyi amfani dasu.

Kasafin naira tiriliyan 47.90 da Shugaba Bola Tinubu ya gabatar wa majalisa a Disambar bara, an ware tiriliyan 4.91 ga bangaren tsaro domin ingata ayyukan jami’an tsaro wajen yaki da ta’addanci.

Bincike ya nuna cewa an ware wa hukumar EFCC naira miliyan N808.7 domin shan mai, sai wasu N462m na ciye-ciye da tande-tande.

Haka kuma gefe guda an ware wa Hukumar DSS naira biliyan N1.37 domin sayen fetur.

Domin samun sauran shirye-shiryen Alfijir labarai/Alfijir news zaku iya bibbiyarmu ta 👇

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

https://www.threads.net/@alfijirlabarai

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

Alfijir labarai Alfijir News Whatsapp Group 👇👇

https://chat.whatsapp.com/ELQRQyq1zGn7zpAVP8DwNj

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *