Babbar Kwamishiniya Mai Kulada Kungiyoyi a Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Jihar Kano KANSIEC, Hajia Amina Inuwa Fagge ta yaba tare da taya Gwamna Abba Kabir Yusuf murnar cika shekaru 62 a duniya.
A wata ganawa da tayi da Jaridar Alfijir, Uwargida Hajiya Amina Fagge ta bayyana jin dadinta bisa irin goyon baya da jajircewar da Gwamna Yusuf keyi na ci gaban jihar, inda ta bayyana salon shugabancinsa a matsayin wani muhimmin al’amari na kawo sauyi mai kyau a jihar.
A cewar Fagge Gwamna Yusuf ya samar musu da isassun kayan aiki don tabbatar da ingancin zaben kananan hukumomi na 2024 da aka gudanar a kananan hukumomi 44, ba tare da wani katsalandan ba.
“Wannan yunƙuri ya nuna irin sadaukarwar sa na tabbatar da gaskiya da rikon amana da kuma shugabanci na gari. A cewar kwamishiniyar
“A bayyane yake karara, baiwa Hukumar zabe KANSIEC ‘yancin gudanar da zabe, Da Gwamna Yusuf ya yi, ya nuna irin amincin sa ga hukumar tare da ba ta cikakkun kayan aiki don Inganta cigaban dimukradiyya.
“Tabbas Gwamnatin Kano karkashin Gwamna Yusuf na samar da gagarumin ci gaba cikin gaggawa wajen yaki da cin hanci da rashawa, tare da tabbatar da hukumomi irin su KANSIEC suna gudanar da ayyukansu ba tare da tsoma bakin kowa ba.
Acewar kwamishiniyar, wannan mataki na tabbatar da dimokuradiyya da bada fifiko don inganta harkar ilimi a jihar Kano, tare da samar da isassun kayan aiki ga matakin firamare har zuwa manyan makarantu abun a yaba ne.
Uwargida Hajiya Amina ta yabawa salon shugabancin Gwamna Yusuf, inda ta ce yunkurinsa na tabbatar da gaskiya, rikon amana, da shugabanci abin kwatance.
A yayin da Gwamna Yusuf ke bikin murnar cika shekaru 62 a duniya, Hajiya Amina Fagge ta yi addu’ar Allah ya kara masa lafiya kwarin gwiwa da basirar cigaba da hidimtawa al’ummar jihar Kano.