Wata Sabuwar! Wai shin da gaske ne ƙungiyar Illuminati ce take ‘juya’ duniya a ɓoye?

IMG 20250316 002724

An shafe shekaru ana bayanin cewa ƙungiyar ‘Illuminati’ a asirce tana jan ragamar al’amuran duniya tare da kafa dokoki.

Hakan ya samo asali ne daga wani abu da ake tunanin ya faru a Turai cikin shekarun 1960.

Zamanin wayayewar kai, daɗaɗɗen lokaci ne da ya faru a ƙarni na 17 da 18 wanda ya haifar da manyan sauye-sauye game da tunani da kimiyya da al’umma musamman a Turai.

Ana alaƙanta Jamus a matsayin tushen Illuminati.

Akwai wata ƙungiya mai abubuwan almara da ake kira Bavarians. An kafa ta a 1776.

Mutane masu ilimi sun haɗu sun soki yadda ƙungiyar ke tafiyar da al’amuranta.

Kamar sauran ƙungiyoyin asiri da ake kira freemasons, ita ma Illuminati ana kallon ta a matsayin wadda za ta bunƙasa.

Sai dai ƴan Conservative da masu suka Kirista, sun nuna adawa.

An daina jin amonsu na wani lokaci inda suka sake dawowa a shekarun 1960.

David Bramwell, wanda ya yi bincike kan ƙungiyar Illuminati, ya ce ƙungiyar Illuminati ta yanzu ta bambanta daga ƙungiyar asiri ta Bavaria.

Lokaci ne da wata tafiya da ke sukar al’adu, ke bazuwa a yammacin duniya.

A lokacin, an buga wani littafi mai suna ‘Principia Discordia’.

Littafin ya yi iƙirari cewa mutane na son zama ƙarƙashin tsarin waɗanda ba su da ƙasa inda suke bauta wa Uwargijiyar tashin hankali mai suna Iris.

Ya yi bayani kan irin rayuwar wahala da wata ƙungiya ke ciki da ke neman tayar da zaune tsaye.

Ɗaya daga cikin marubutan littafin shi ne Anton Wilson.

Yana tunanin “duniya ta zama kama-karya. sai ya emi kawo sauyi ta hanyar ingiza tashin hankali.

“Yana ganin za a iya kawo sauyi ta hanyar amfani da kafafen yaɗa labarai, da yaɗa labaran ƙarya,” in ji David Bramwell, wanda ya yi bincike kan Illuminati.

Marubucin, tare da abokinsa sun buga wata wasiƙar bogi a mujallar Playboy, da sunan ta fito ne daga masu karatu.

Wasiƙar ta bayyana kasantuwar wata ƙungiyar asiri da ake kira Illuminati.

Wata hanya ce da za ta sa mutane shakku kan ko abin da suke ji ko karantawa gaskiya ne.

Sai mutane da dama suka fara yadda da Illuminati.

Ana tunanin Illuminati ce ke kitsa abubuwa da dama da ba a sani ba, har da wanda ya kashe John F. Kennedy?

An amince da littafin da ya sa raɗe-raɗin suka bazu inda kuma ya zama ana nuna labarin a Liverpool da ke Ingila.

Lokacin da aka wallafa littafin ‘When playing cards for a game a shekarar 1975, hotunan da galibi ake alaƙanta su da ƙungiyar sun yi shura.

A yanzu, ana tunanin fitattun mawaƙa irin su Jay Z da Beyonce ƴan Illuminati ne.

Sun fi samun tagomashi a duk lokacin da suka yi waƙa kan dandamali mai kusurwa uku.

Duk da cewa hakan ba gaskiya bane, har yanzu ana yayata ra’ayin wasu game da wasu bayanai na shekarun 1960.

Ana yayata irin waɗannan shaci-faɗin a shafuka irinsu 4chan da Reddit.

A cewar ƙuri’ar jin ra’ayin jama’a da aka gudanar a 2025 a Amurka, rabin al’ummar ƙasar sun yadda da aƙalla guda cikin shaci-faɗin.

A cewar Viren Swamy, da ke aiki a Jami’r Abglia Ruskin, mutane na iya yadda da bayanan tsare-tsaren saboda dalilai da dama.

Akwai ƙwararru da ke ganin watakila suna da matsala a lafiyar ƙwaƙwalwarsu.

Wasu kuma sun ce mutane za su fi son taƙaitacciyar amsa ko bayani kan wani shaci-faɗi a maimakon gaskiyar da ke raunana ƙwarin gwiwa.

Binciken da aka yi a baya-bayan nan ya nuna cewa mutane masu ilimi ba su yadda da irin waɗannan bayanan ba.

A cewar ƙwararren, gwamnatoci a ƙasashen Kudancin Asiya ne suka fi amfani da irin waɗannan bayanan domin samun iko da al’umma.

A yammacin duniya kuma, idan mutane suka ji sun rasa goyon baya ko wakilci, sai su rungumi bayanan na shaci-faɗi.

Akwai rahotanni da ke cewa Shugabanni kamar Donald Trump suna yayata irin waɗannan bayanai na ra’ayin jama’a.

Misali akwai iƙirarin cewa ba a haifi Barack Obama ba a Amurka sai kuma iƙirarin cewa an tafka maguɗi a zaɓen da Joe Biden ya yi nasara.

Mutanen da ba su yadda da irin waɗannan soki burutsun ba, ba su cika aminta da kafafen yaɗa labarai ba.

An ba da rahoton cewa Trump ya ce zai wakilci mutanen da masu galihu suka watsar,

A cewar David Bremwell, mai nazari kan Illuminati, mutumin da ya farfaɗo da Illuminati a littafinsa na shekarun 1960 watakila ya sha mamakin ganin yadda shaci-faɗi suka yi suna.

Ƙwararru sun yi hasashe cewa yaƙin kawar da labaran ƙarya da ƙaruwar mutane a ƙungiyoyin da ke ɗiga ayar tambaya kan gaskiyar bayanan da aka wallafa a shafukan sada zumunta zai shafi bayanan da suka shafi Illuminati.

Asalin Illuminati
Illuminati ta samo asali shekaru 200 da suka gabata.

Sister Anna na aiki a majami’ar Gothic.

Ta san cewa mutane daga Faransa da Ingila da wasu ƙasashe suna zuwa wurin domin gudanar da taruka sai dai ba ta da cikakken bayani game da inda suke.

Sister Anna, wadda ke aiki a shagon sayar da litattafai na cocin, ta j labari cewa akwai taron ƴan Illuminati a Bavaria.

Duk da cewa birnin Ingolstadt ne mahaifar Illuminati, taron da ake a asirce ba gaskiya ba ne.

A shekarar 1776, Adam Weissput, wani farfesa a shari’a daga jami’ar Ingolstadt, ya kafa Illuminati.

An tsara ta ne domin haɗa masana wuri ɗaya masu bayyana ra’ayinsu ba tare da tsoro ba. Baya ga ƙungiyar Freemason, ita ma ta samu tasiri daga masanan falsafa na Faransa.

An kafa ta ne da nufin samar da wata ƙungiyar masana ba wai ƙungiyar addini ba.

Ba abu ne mai sauƙi a samar da wani tunani a birnin da aka rungumi addini.

IlluminatiAsalin hoton,volkerpreusser/Alamy
Da farko ya zaɓi biyar daga cikin ɗalibansa masu hazaƙa ya sa su a ƙungiyar.

Daga baya, ƙungiyar ta fara samun karɓuwa.

Yayin da mambobinta ke yaɗa aƙidarsu, suna kuma da bayanai na sa ido kan ayyukan gwamnati da cibiyoyin addini.

Sun yi ƙoƙarin yaɗa fahimtarsu ta hanyar tara dukiya.

Fitaccen jami’in diflomasiyyar Jamus, Baron Adolf yana daga cikin waɗanda suka assasa tunanin.

Yawan mambobinsu a Bavaria da Faransa da Hungary da Italiya da Poland sun kai dubu biyu.

Ɗanjarida Micheal Kleiner ya kira wanda ya ƙirƙiri Illuminati a matsayin mai juyin juya hali.

“Ya koya wa mutane yadda za su inganta rayuwarsu. Yana son ya gyara al’umma. Yana son a samu kyakkyawar al’umma da gwamnati mai nagarta,” in ji shi.

Saɓanin abin da ake bayar da dama a jami’a inda ya koyar, yana ganin ya kamata a yi duk wata koyarwa ta hanyar ilimi.

An tarwatsa ƙungiyar yayin da suke gudanar da zanga-zangar adawa da gwamnati shekara 10 bayan kafa ta kuma wanda ya kafa ta ya tsere zuwa birnin Gotha.

Sai dai, masana tarihi sun ce har yanzu akwai mutane da suke ganin ba a haramta ƙungiyar ba.

A cewar Dakta Micheal Wood, wanda yake aiki a jami’ar Winchester, Illuminati ra’ayoyin mutane ne ɗauke da sirrika.

A cewar Maria Ephlischmer, wadda ke aiki a gidan ajiyar kayan tarihi ta ce gidan tarihin yana da litattafai kan Illuminati da ke da alaƙa da abubuwan da suka faru a duniya.

Illuminati textsAsalin hoton,Julie Ovgaard
A cewar Klarner, wanda ya je birnin, ya ga baƙi waɗanda suka yadda da irin waɗannan bayanan.

“Yadda Illuminati take a yanzu abin ban sha’awa ne. Ta sha bamban da Illuminati ta gaske,” in ji shi.

Sister Anna ta ce mutanen da suka yadda ana yin taron Illuminati a birnin sun tambaye ta game da wurin duk da cewa ba gaskiya ba ne.

Akwai mutane da dama da suka yadda cewa Illuminati ce ke da alhakin haifar da juyin juya halin Faransa da hare-haren 11 ga watan Satumba da aka kai kan Amurka da sauran muhimman al’amura da suka faru.

BBC

Domin samun sauran shirye-shiryen Alfijir labarai/Alfijir news ku shiga nan  👇

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

https://www.threads.net/@alfijirlabarai

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

Alfijir labarai Alfijir News Whatsapp Group 👇👇

https://chat.whatsapp.com/KoLt2IMlnQfJPP6zNrcNKD

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *