Kungiyoyin kwadago a jihar Rivers sun yi barazanar daukar matakan hadin gwiwa na kungiyoyin kwadago da ka iya hana gudanar da harkokin tattalin arziki na kasa, idan Shugaba Bola Tinubu bai janye dokar-ta-bacin da aka sanya a jihar ba.
A wata sanarwa da shugabannin kungiyar kwadago ta Najeriya (NLC) da kungiyar hadin gwiwar kwadago (TUC) a Rivers suka sanya wa hannu, kungiyoyin sun bayyana cewa dokar ta-baci ta shafi biyan albashin ma’aikata.
Kungiyoyin kwadago sun ce ma’aikatan kananan hukumomi da har yanzu ba su karɓi albashinsu ba, sun shiga cikin mawuyacin hali na tattalin arziki.
Haka kuma, kungiyoyin sun bayyana cewa ayyana dokar ta-baci ya jefa jihar cikin wani yanayi , inda masu zuba jari da suka nuna sha’awar shirin “New Rivers Vision” suka janye hannayensu daga zuba jari a jihar.
Domin samun sauran shirye-shiryen Alfijir labarai/Alfijir news ku shiga nan 👇
https://twitter.com/Musabestseller?s=09
https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165
https://www.threads.net/@alfijirlabarai
https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12
https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag
Alfijir labarai Alfijir News Whatsapp Group 👇👇
https://chat.whatsapp.com/KoLt2IMlnQfJPP6zNrcNKD