Hukumar Hisbah ta Jihar Kano ta yi alla-wadai da wata shahararriyar wakar Hausa mai taken “Amana ta” da mawaki Hamisu Breaker ya rera, inda ta shawarci matasa da su guji sauraren wakar.
Hisbah ta nuna fushin ta kan wakar ta bakin Dr. Khadija Sagir, Mataimakiyar Kwamanda Janar ta Hisbah mai kula da harkokin mata.
Ta bayyana cewa wakar na dauke da abubuwan da ke karfafa aikata alfasha, musamman yadda mata ke rawa da kuma amfani da kalmomin batsa a cikin bidiyon wakar.
Dr. Khadija ta kara da cewa bisa abinda ke cikin wakar, an dauke ta a matsayin haramun a karkashin koyarwar addinin Musulunci.
Hamisu Breaker sananne ne a fagen wakokin Hausa, inda ya shahara wajen amfani da baituka masu ma’ana da karin maganganu na gargajiya. Wakokinsa da dama.
Domin samun sauran shirye-shiryen Alfijir labarai/Alfijir news ku shiga nan 👇
https://twitter.com/Musabestseller?s=09
https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165
https://www.threads.net/@alfijirlabarai
https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12
https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag
Alfijir labarai Alfijir News Whatsapp Group 👇👇
https://chat.whatsapp.com/KoLt2IMlnQfJPP6zNrcNKD