Hisbah  ta yi alla-wadai da wakar Hamisu Breaker ta “Amana ta”

IMG 20250424 124215

Hukumar Hisbah ta Jihar Kano ta yi alla-wadai da wata  shahararriyar wakar Hausa mai taken “Amana ta” da mawaki Hamisu Breaker ya rera, inda ta shawarci matasa da su guji sauraren wakar.

Hisbah ta nuna fushin ta kan wakar ta bakin Dr. Khadija Sagir, Mataimakiyar Kwamanda Janar ta Hisbah mai kula da harkokin mata.

Ta bayyana cewa wakar na dauke da abubuwan da ke karfafa aikata alfasha, musamman yadda mata ke rawa da kuma amfani da kalmomin batsa a cikin bidiyon wakar.

Dr. Khadija ta kara da cewa bisa abinda ke cikin wakar, an dauke ta a matsayin haramun a karkashin koyarwar addinin Musulunci.

Hamisu Breaker sananne ne a fagen wakokin Hausa, inda ya shahara wajen amfani da baituka masu ma’ana da karin maganganu na gargajiya. Wakokinsa da dama.

Domin samun sauran shirye-shiryen Alfijir labarai/Alfijir news ku shiga nan  👇

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

https://www.threads.net/@alfijirlabarai

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

Alfijir labarai Alfijir News Whatsapp Group 👇👇

https://chat.whatsapp.com/KoLt2IMlnQfJPP6zNrcNKD

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *