Yadda Matasan yan mata suka fitar da Najeriya kunya a idon Duniya

IMG 181238 05825 1754413974259

Al ummar Najeriya musamman Jihar Yobe na cike da farin ciki bayan ‘yan mata biyu masu hazaka sun kafa tarihi a matakin duniya, inda suka lashe manyan kyaututtuka a gasar 2025 na Teen Eagle Global Finals da aka gudanar a birnin London.

Rukayya Fema ta lashe kambun Mafi Ƙwararewa a Muhawara (Overall Best Debater), yayin da Nafisa Aliyu ta zama Zakara a Gasar Spelling Bee.

Dukkanin su dalibai ne a makarantar Yobe Tulip International College (NTIC), in da suka nuna bajinta, ladabi, da jarumta ta musamman.

Nasara ta biyu ba wai kawai ta kawo ɗaukaka ga Jihar Yobe ba, har ma ta haskaka ƙwarewar ilimin Najeriya a idon duniya.

Mai kula da harkokin UN Women ga Gwamnan Jihar Yobe, Mai Mala Buni Hon. Fatima Muhammad Paga, ta taya matasan murnar wannan nasara tare da yin kira da a girmama su a matakin ƙasa, iri ɗaya da yadda ake yi wa taurarin wasanni kamar Super Falcons.

Fatima Paga, tace waɗannan ‘yan mata biyu sun ɗaga martabar Yobe da Najeriya zuwa matakin duniya.

Hakan yasa tace sun cancanci a ba su lambar yabo da $100,000 da kuma babban biki na girmamawa a Abuja, kamar yadda aka yiwa jaruman wasanni.

Rukayya da Nafisa sun tabbata jarumai a fannin ilimi suke da damar samun irin wannan yabo da tallafi,” in ji Hon. Fatima Paga

Ta kuma yi kira ga al’ummar Yobe da ‘yan Najeriya baki ɗaya da su mara wa zakarun baya, tare da amfani da nasarar su a matsayin kuzari ga ƙarin ‘yan mata su ma su yi fice a fagen ilimi a duniya.

Wannan nasara ta Rukayya da Nafisa ba kawai nasara ce ta kashin kai ba, alama ce ta fata, juriya, da kuma irin ƙarfin da matasan Najeriya za su iya cimmawa idan aka ba su kyakkyawan damar ilimi da ƙarfafawa.

Ga masu son bada talla ko shawarwari a kira wannan lambar +2348032077835

Domin samun sauran shirye-shirye Alfijir labarai/Alfijir news ku biyo mu ta nan 👇

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

https://www.threads.net/@alfijirlabarai

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

Alfijir labarai Alfijir News Whatsapp Group 👇👇

https://chat.whatsapp.com/H5oBRaZBdCVIyOTIV5eMfb?mode=ac_t

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *