Gwamnatin Najeriya ta fara korar bakin haure 192 zuwa ƙasashen su bayan Samunsu da aikata laifuka

FB IMG 1755497881977

Hukumar Kula da Shige da Fice ta Najeriya (NIS) ta fara korar bakin haure 192 da aka same su da laifin damfara ta yanar gizo a kasar.

Alfijir labarai ta rawaito cewa rukuni na farko na bakin hauren guda 42 an korar da su ranar Lahadi, yayin da wani rukuni zai tashi ta jirgin sama zuwa kasashensu daban-daban ranar Litinin da Talata.

A watan Disamba 2024, Hukumar Yaki da Cin Hanci da Rashawa ta Najeriya (EFCC) ta cafke mutane 792 daga wata kungiya da ake zargi da damfarar cryptocurrency da kwaikwayon soyayya.

An cafke wadanda ake zargi a wani gini mai hawa bakwai a Victoria Island, Lagos. An ce bakin hauren suna amfani da ginin don “koyar da ‘yan Najeriya yadda ake shirya damfaran soyayya da zuba jari.”

Daga cikin ‘yan kungiyar akwai ‘yan kasar Sin 114, ‘yan Philippines 40, biyu ‘yan Khazartan, daya daga Pakistan, da daya daga Indonesia.

Hukumar yaki da rashawa ta bayyana wannan aiki a matsayin “cikakken kamawa mafi girma na damfaran yanar gizo a kasar a rana guda.”

EFCC ta gurfanar da wadanda ake zargin a kotun tarayya dake Lagos.
A watan Yuni, wasu daga cikin bakin hauren aka same su da laifi a kotu.

Kotu ta kuma umurci kwantirola janar ta Hukumar Kula da Shige da Fice ta Najeriya (NIS) da ya mayar da bakin hauren kasarsu cikin kwanaki bakwai bayan sun kammala zaman kurkuku.

A watan Yuli, EFCC ta tabbatar da karbar kadarorin dijital na kimanin dala $222,729 da aka kama daga wasu ‘yan kasar Sin da aka gurfanar yayin aikin kamawa.

The Cable

Ga masu son bada talla ko shawarwari a kira wannan lambar +2348032077835

Domin samun sauran shirye-shirye Alfijir labarai/Alfijir news ku biyo mu ta nan 👇

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

https://www.threads.net/@alfijirlabarai

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

Alfijir labarai Alfijir News Whatsapp Group 👇👇

https://chat.whatsapp.com/H5oBRaZBdCVIyOTIV5eMfb?mode=ac_t

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *