Asibitin Kwararru na Best Choice ya sake bijiro da wasu ayyukan farantawa al’umma bayan bude fayil kyauta da rage kaso 50% cikin ayyukansu da suka fara a satin da ya gabata.
Yanzu haka asibitin ya sake tanadar kwararrun likitoci masu yin wadannan Tiyatar
( Urology) Aikin Mafitsara
(Hynea) Qabar ciki
(Orthopaedic) Aikin Qashi,
(ENT) Aikin Hanci , Makogaro da Kunne
(Dental) Hakori
(Fibroid) Qarin mahaifa,
(Urology) Aikin Mafitsara
Asibitin ya zakulo zakakuran likitoci domin gudanar da wannan ayyukan daga yau Litinin 8, ga watan Yuli 2025, ga duk masu bukatar wannan ayyukan, akan farashin kaso 50% cikin 100 shima za a biya.
Hakan na kunshe ne cikin wata sanar da shugaban asibitin Alh Auwal Muhd Lawal ya bayyanawa jaridar Alfijir Labarai a safiyar Litinin.
Lawal yace sun yanke wannan hukuncin ne sakamakon buƙatar da al’umma suke da ita a wannan bangarorin ga kuma yawan da mutane suka yiwa gwamnati shi yasa hukumar gudanarwar Asibitin Kwararru na Best Choice itama taga da cewar bada tata gudummawar domin kara karfafar gwamnati a wannan fannin.
Auwal ya kuma bayyana jin dadinsa ganin yadda al’umma suke ta cin gajiyar bude fiyil kyauta da rage kaso 50% ganin likita tare da manya da kananan ayyukan asibitin da yayi a satin da ya gabata.
Dukkannin waɗannan ayyuka za a fara gudanar da sune a yau Litinin, don haka ga masu irin wadannan matsaloli za su iya zuwa domin a tantancesu.
Asibitin Kwararru Na Best Choice yana nan a mazauninsa na dindindin dake Plot 782/783 tal’udu kusa da makarantar Sheikh Bashir Eli Rayya kuma muna aikinmu ba dare ba rana tare da manyan likitoci.Za a iya tuntubar mu ta yanar gizo bestchoiceclinic@gmail.combestchoiceclinic@yahoo.comKo facebook Best Choice Specialist HospitalKo kira da whatsapp akan +2347034951671+234912 345 3534+2342082443318
Ga masu son bada talla ko shawarwari a kira wannan lambar +2348032077835
Domin samun sauran shirye-shirye Alfijir labarai/Alfijir news ku biyo mu ta nan 👇
https://twitter.com/Musabestseller?s=09
https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165
https://www.threads.net/@alfijirlabarai
https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12
https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag
Alfijir labarai Alfijir News Whatsapp Group 👇👇
https://chat.whatsapp.com/H5oBRaZBdCVIyOTIV5eMfb?mode=ac_t