Kano ta samu kujeru 5,684 don aikin Hajji na 2026, hukumar ta fitar da kuɗin ajiya

FB IMG 1756980849599

Shugaban Hukumar Jin Dadin Alhazai ta Jihar Kano, Lamin Rabi’u Danbappa, ya sanar da kudin ajiya na aikin Hajji na shekarar 2026 bisa umarnin Hukumar Alhazai ta Ƙasa (NAHCON).

Lamin ya bayyana hakan ne yayin taro da mambobin hukumar, jami’an gudanarwa, da kuma jami’an Alhazai na kananan hukumomi a ofishinsa.

Ya ce NAHCON ta amince da naira miliyan takwas da rabi (₦8,500,000) a matsayin kudin ajiya ga duk mai niyyar zuwa aikin Hajji a shekarar 2026. Hukumar za ta karɓi kudaden ne ta hanyar banki ta hannun jami’an Alhazai na kananan hukumomi.

Haka kuma, ya bayyana cewa Jihar Kano ta samu kujeru 5,684 don aikin Hajji na 2026. Ya ce an fara karɓar kudaden ajiya daga yanzu, kuma za a ci gaba da karɓa har zuwa 5 ga Oktoba, 2025, ranar da za a fitar da cikakken kudin aikin Hajjin 2026.

A wata sanarwa da jami’in hulda da jama’a na hukumar Sulaiman Abdullahi Dederi ya aikewa manema labarai ya ce, Shugaban hukumar ya shawarci duk masu niyyar zuwa aikin Hajji su gaggauta biyan kudaden ajiya domin bin jadawalin da Saudiyya ta tanada.

Ya kuma jaddada cewa dole ne duk mai neman zuwa aikin Hajji ya kawo hotuna guda takwas (passport size) da fasfo na ƙasa da ƙasa mai inganci.

A nasa jawabin, Shugaban Kwamitin Gudanarwa na hukumar, Yusif Lawan, ya yi addu’a ga Allah ya ba wa duk masu niyyar zuwa aikin Hajji damar biyan kuɗin cikin sauƙi.

Ya kuma umarci jami’an Alhazai na kananan hukumomi da su yi aiki tukuru wajen tabbatar da cewar kowace karamar hukuma ta samu kujerun da aka ware mata yadda ya kamata.

Ga masu son bada talla ko shawarwari a kira wannan lambar +2348032077835

Domin samun sauran shirye-shirye Alfijir labarai/Alfijir news ku biyo mu ta nan 👇

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

https://www.threads.net/@alfijirlabarai

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

Alfijir labarai Alfijir News Whatsapp Group 👇👇

https://chat.whatsapp.com/H5oBRaZBdCVIyOTIV5eMfb?mode=ac_t

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *