Hukumar kula da abinci da magunguna ta ƙasa NAFDAC ta rufe manyan kantunan ƴan China biyu da ke yankin Jabi, Abuja saboda karya dokar siyar da kayayyaki a Najeriya.
Hukumar ta kuma rufe shagunan kayan kwalliya guda takwas a kasuwar Wuse.
Hukumar ta bayyana hakan a wata sanarwa da ta fitar ranar Jumma’a kamar yadda jaridar The Punch ta ruwaito.
Hukumar ta kuma ce ta rufe kantunan ne bisa umarnin shugabar hukumar, Prof. Mojisola Adeyeye.”
“Manyan kantunan waɗanda ke a Jabi, an rufe su ne bayan samun ƙorafe-ƙorafe daga masu saye da amfani da kayayyakinsu da kuma binciken da tawagar hukumar ta yi.”
“Binciken da ƙorafe-ƙorafen sun nuna cewa masu kantunan suna sayar da kayan abincin da ba a yi rijistarsu ba da kuma kayayyakin da laƙabinsu kawai a harshen China ne wanda ya saɓawa ƙa’idar NAFDAC wadda ke bukatar fassarar turanci domin masu saye da hukuma su fahimta.
BBC
Ga masu son bada talla ko shawarwari a kira wannan lambar +2348032077835
Domin samun sauran shirye-shirye Alfijir labarai/Alfijir news ku biyo mu ta nan 👇
https://twitter.com/Musabestseller?s=09
https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165
https://www.threads.net/@alfijirlabarai
https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12
https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag
Alfijir labarai Alfijir News Whatsapp Group 👇👇
https://chat.whatsapp.com/H5oBRaZBdCVIyOTIV5eMfb?mode=ac_t