Duk Nisan Jifa: An ba da belin dan Gaddafi bayan da ya shafe shekaru 10 a tsare a Lebanon

IMG 142741 111125 1762867693621

Dan Gaddafi ya yi niyya ya bar Lebanon zuwa wani wuri na “sirri”, a cewar lauyansa, yana mai cewa yana da fasfo din Libya.

Lebanon ta saki Hannibal Gaddafi, É—an tsohon shugaban Libya Muammar Gaddafi, bisa sharadin beli, bayan da ya shafe kusan shekaru goma yana É—aure a kurkuku, in ji lauyansa.

“Mun bar wurin, yanzu ya samu yanci,” in ji Laurent Bayon a ranar Litinin, awanni kaÉ—an bayan an biya kudin beli har dala 900,000.

Ana zargin Hannibal Gaddafi mai shekaru 49 da boye bayanai game da bacewar limamin Shi’a na Lebanon Mussa Sadr a Libya a 1978, amma ba a taba gurfanar da shi a kotu ba.

A lokacin batan Sadr, Hannibal yana da shekaru biyu.

“An biya jinginar ne da safiyar yau,” in ji Lauya Bayon kamar yadda ya fada tun da fari a ranar Litinin. “A karshe Hannibal Gaddafi zai sami yanci. Wannan shi ne Æ™arshen wani mafarki mai muni da ya É—auki shekaru 10 a rayuwarsa.”

A watan Oktoba, wani alkalin kotu ya umurci a saki Gaddafi idan an biya jinginar dala miliyan 11, wanda aka rage zuwa $900,000 makon da ya gabata bayan Æ™orafin tawagar kare shari’a.

Wata majiya a bangaren shari’a a Lebanon ta tabbatar a ranar Litinin cewa an biya jinginar, kuma tawagar lauyoyinsa na kammala tsare-tsaren sakin sa.

Bayan ya ce wanda yake karewa zai bar Lebanon zuwa wani wuri ‘na sirri’, ya kuma ce yana da fasfo na Libya.

TRT Afrika Hausa.

Ga masu son bada talla ko shawarwari a kira wannan lambar +2348032077835

Domin samun sauran shirye-shirye Alfijir labarai/Alfijir news ku biyo mu ta nan 👇

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

https://www.threads.net/@alfijirlabarai

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

Alfijir labarai Alfijir News Whatsapp Group 👇👇

https://chat.whatsapp.com/H5oBRaZBdCVIyOTIV5eMfb?mode=ac_t

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *