Daga Aminu Bala Madobi
An wayi gari da tashin hankali bayan da wasu ‘yan mata, waɗanda ake zargin ƙawayen wata budurwa ne mai suna Fatima, suka farfasawa wani saurayi Lukman bulo (blocks) sama da 170 a daren jiya, sakamakon fasa neman auren da ya yi wa ƙawarsu bayan shafe tsawon shekaru shida suna soyayya.
Rahotanni sun bayyana cewa Lukman ne ya yanke shawarar janye neman auren Fatima, inda ya ce tana yi masa “tsufa sosai” kuma ba ta jin maganarsa.
A cewarsa, yanzu burinsa shi ne ya nemi ƙaramar yarinya mai shekaru 18 zuwa 19, wacce zai ce za ta kula da shi tare da share masa hawayensa a cikin gidansa.
Wannan mataki na Lukman ya fusata ƙawayen Fatima matuƙa, inda suka bayyana cewa abin da ya yi cin amana ne da raini bayan dogon lokacin soyayya da alkawurra da aka sha. Sun zargi saurayin da watsi da ƙawarsu ba tare da la’akari da shekarun da suka ɓata tare ba.
A sakamakon haka, a daren jiya ƙawayen budurwar suka kai hari wurin da Lukman ya tara bulo, inda suka lalata su gaba ɗaya.
Har zuwa lokacin haɗa wannan rahoto, ba a tabbatar da ko an kai ƙarar lamarin ga jami’an tsaro ba, yayin da al’umma ke ci gaba da tofa albarkacin baki kan abin da ya faru
For advertisement or further advisory services, the public has been directed to contact +2348032077835.
For more information about Alfijir labarai/Alfijir news Fallow here 👇
https://twitter.com/Musabestseller?s=09
https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165
https://www.threads.net/@alfijirlabarai
https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12
https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag
Alfijir labarai Alfijir News Whatsapp Group 👇👇
https://chat.whatsapp.com/H5oBRaZBdCVIyOTIV5eMfb?mode=ac_t