Daga Auwal Tuhami Zarewa
Kasuwar Damboa ta nuna sauye-sauye a farashin kayan gona a wannan makon. Wasu kayan sun ƙara farashi yayin da wasu suka ci gaba da kasancewa a daidai matsayi.
HATSI DA KAYAN ABINCI
Masara (100kg) — ₦28,000
Dawa (100kg) — ₦26,000
Shinkafa (60kg) — ₦33,000
WAKE DA GYAƊA
Wake ruwan kasa Banjara (75kg) — ₦70,000
Jan Wake (85kg) — ₦62,000
Gangala (50kg) — ₦41,000
Gyaɗa Sadiya (80kg) — ₦85,000
Gyaɗa Kamfala (85kg) — ₦90,000
YANAYIN KASUWA
Masara da dawa sun ɗan ƙara farashi a kasuwa, yayin da shinkafa ta ci gaba da kasancewa a daidai farashi.
A bangaren wake da gyaɗa, an samu sauye-sauye inda gangala da gyaɗa suka ƙara farashi, yayin da jan wake ya ɗan sauka idan aka kwatanta da makon da ya gabata.
BAYANIN KASUWA
Tashin farashin masara, dawa da gyaɗa na nuna ƙarin buƙata a kasuwa tare da yiwuwar ƙarancin kaya.
Shinkafa kuwa tana nuna daidaiton samuwa da buƙata a kasuwa.
Ga masu son bada talla ko shawarwari a kira wannan lambar +2348032077835
Domin samun sauran shirye-shirye Alfijir labarai/Alfijir news ku biyo mu ta nan 👇
https://twitter.com/Musabestseller?s=09
https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165
https://www.threads.net/@alfijirlabarai
https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12
https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag
Alfijir labarai Alfijir News Whatsapp Group 👇👇
https://chat.whatsapp.com/H5oBRaZBdCVIyOTIV5eMfb?mode=ac_t