Gwamna Abba Kabir Yusuf Ya Nada Sarkin Gaya Amirul Hajjin Bana

FB IMG 1778588658214

Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya amince da nadin Sarkin Gaya, Alhaji Dr. Aliyu Ibrahim Abdulkadir, a matsayin Amirul Hajj na jihar domin jagorantar aikin Hajjin shekarar 2026.

Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan, Sunusi Bature Dawakin Tofa, ya fitar a ranar Talata.

Sanarwar ta kuma bayyana cewa Sarkin Karaye, Mai Martaba Alhaji Muhammad Muhammad Maharaz, an nada shi a matsayin Mataimakin Amirul Hajj.

Gwamnatin jihar ta bayyana cewa ana sa ran hukumar jin dadin Alhazai ta Jihar Kano za ta bayar da cikakken hadin kai da goyon baya ga Amirul Hajj da mataimakinsa domin tabbatar da gudanar da aikin hajjin cikin nasara da kwanciyar hankali.

Haka kuma gwamnatin ta yi wa Amirul Hajjin da mataimakinsa da ma’aikatan hukumar jin dadin Alhazai ta jihar fatan alheri tare da addu’ar Allah ya ba maniyyatan jihar damar gudanar da aikin Hajji karbabbe tare da dawowa gida lafiya.

Ga masu son bada talla ko shawarwari a kira wannan lambar +2348032077835

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *