Hukumar Tace Finafinai da Ɗab’i ta Jihar Kano ta sanar da dakatar da jaruman Kannywood biyu, Adam Garba wanda aka fi sani da Raba Gardama da kuma Amina Uba Hassan (Jamila a cikin shirin Labarina), daga gudanar da harkokin fim a jihar na tsawon shekara guda.
Hakan na kunshe cikin wata sanarwa da jami’in yada labaran hukumar, Kwamared Abdullahi Sani Sulaiman ya fitar a madadin shugaban hukumar, Malam Abba El-Mustapha.
Hukumar ta bayyana cewa ta ɗauki matakin ne bayan fitowarsu a sabon fim ɗin Har Abadan, inda ake zargin sun aikata wasu abubuwa da suka saɓa da ƙa’idoji, al’ada da tarbiyyar al’ummar jihar Kano, ciki har da wasu yanayi na taɓa juna a cikin shirin.
Sanarwar da kakakin hukumar ya fitar ta ce dakatarwar za ta fara aiki nan take a duk faɗin jihar Kano.
Shugaban hukumar, Malam Abba El-Mustapha ya yi kira ga ’yan masana’antar Kannywood da su guji duk wani abu da zai zubar musu da mutunci ko kuma ya bata martabar masana’antar. Haka kuma ya gargadi masu shirya fina-finai da daraktoci da su mutunta umarnin dakatarwar, yana mai cewa duk wanda ya ci gaba da aiki da jaruman da aka dakatar tamkar yana kalubalantar dokar hukumar ne kai tsaye.
Ga masu son bada talla ko shawarwari a kira wannan lambar +2348032077835
Domin samun sauran shirye-shirye Alfijir labarai/Alfijir news ku biyo mu ta nan 👇
https://twitter.com/Musabestseller?s=09
https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165
https://www.threads.net/@alfijirlabarai
https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12
https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag
Alfijir labarai Alfijir News Whatsapp Group 👇👇
https://chat.whatsapp.com/H5oBRaZBdCVIyOTIV5eMfb?mode=ac_t