Alfijr ta rawaito gwamnatin tarayya ta hannun hukumar tantance tallace tallace ta ja hankalin marubuta, Masu talla da Barkwanci a yanar gizo, dasu gwggauta yin rijista ko kuma su fuskanci fushin hukumar.
Masu amfani da kafofin watsa labarai na zamani ciki har da masu yaɗa tallace tallace dasu nemi lasisi domin ci gaba da inganta ayyukan su.
Cikin wata sanarwar manema labarai da Darakta-Janar na ARCON Dr Olalekan Fadolapo ya sanya wa hannu ta ce, yawancin tallace-tallacen da mutane suke yadawa basu da lasisin amincewar hukumar.
hukumar kula da tallace-tallace ta kasar ta bayyana fushinta na karya doka “za mu dauki matakan da suka dace da suka hada da sanya takunkumi da kuma gurfanar da wadanda suka karya tanadin dokar don tabbatar da aiki.”
Sanarwar ta kara da cewa, “ARCON ta samu korafe-korafe kan tallace-tallace da ayyukan sadarwar tallan masu wasan barkwanci, masu kirkira da kuma masu rubutun ra’ayi a yanar gizo da dai sauran su.
Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a
Facebook. Best seller Channel
YouTube. Best Seller Channel
Twitter. @Musabestseller
Instagram. @musa_bestseller
Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇