Abduljabbar Kabara Ya Kalubalanci Hukuncin Alkali Sarki Yola A kotu

Alfijr ta rawaito Abduljabbar Shaikh Nasir Kabara wanda Kotu ta zartarwa da hukuncin kisa ta hanyar rataya ya ce bai gamsu da hukuncin da aka yi masa ba gaba daya.

Hakan na kunshe ne cikin wata takarda da lauyansa ya mikawa babbar kotun jihar Kano. Takardar na cewa:

Ni Abduljabbar ban gamsu da hukuncin da Kotun Shari’ar Musulunci ta Kofar Kudu ta yanke a kaina ba, a shari’a mai lamba CR/01/2021 da aka zartar ranar 15th December, 2022, ƙarƙashin Alkali Ibrahim Sarki Yola.
Abduljabbar ya daukaka kara zuwa babbar kotun jihar kano bisa dalilin da ya bayyana a sakin layi na 3 na takardar daukaka ƙarar.

Cikin takardar yace bai yarda da Dukkan hukuncin da karamar kotun ta yanke masa ba.

Ya kuma bukaci kotun daukaka kara da ta yi la’akari da duk bukatun da ya bayyana a sakin layi na 4 na wannan takardan daukaka kara.

Abduljabbar din ya cigaba da bayyana cewa ya bayyana sunayen duk wadanda wannan roko ya shafa kai tsaye a sakin layi na 5 na takardan daukaka kara.

Har ila yau ya bayyana cewa hukuncin da aka yi masa ya saɓa da tanadin da dokar Shari’a ta shekara ta 2000 ta jihar Kano tayi.

Ita dai kotun shari’ar Muslunci dake kofar kudu ta baiwa Abduljabbar da gwamnatin Kano kwanaki 30 daga 15/12/22 domin daukaka kara ga wanda bai gamsu da hukuncin nata ba

Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a

Facebook. Best seller Channel
YouTube. Best Seller Channel
Twitter. @Musabestseller
Instagram. @musa_bestseller

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇

https://chat.whatsapp.com/H5oBRaZBdCVIyOTIV5eMfb

2 Replies to “Abduljabbar Kabara Ya Kalubalanci Hukuncin Alkali Sarki Yola A kotu

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *