Alfijr ta rawaito Mai martaba sarkin kano Alhaji Aminu Ado Bayero ya bayyana irin gudumawar da likitoci suke bayarwa wajen cetan rayukan al’umma da cewa aikine na sadaukar da rayuwa.
Sarkin ya bayyana haka ne lokacin da yake karbar bakuncin shugabanin kungiyoyin likitoci kwararru mata dana kungiyar likitoci masu lura da cutar koda ta kasa yayin da suka ziyarce shi a fadar sa.
Ya kara da cewa aikin da likitoci suke aikine da yake ceton rayuwar al’umma ne duba da yanayin da likitocin suke karbar mara lafiya a lokutan da aka kaishi asibiti.
Ya kuma ce su cigaba da godewa Allah bisa ni’imar da yayi musu wajen samun ilimin cetan rayuwar al’ummar kasar nan.
Da yake jawabin Shugaban sashin kula da masu fama da ciwon koda na asibitin koyarwa na malam Aminu Kano farfesa Aliyu Abdu ya ce, sun ziyarci fadar sarkin ne domin neman albarka duba da taron da zasu gudanar na shekara shekara anan jihar Kano.
Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a
Facebook. Best seller Channel
YouTube. Best Seller Channel
Twitter. @Musabestseller
Instagram. @musa_bestseller
Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇