Gwamnan Babban Bankin Najeriya Ya Mayarwa Da Ganduje Martani

Alfijr ta rawaito Godwin Emefiele wanda ke zaman gwamnan babban bankin kasa CBN, yace bai fahimci alakar batun sauyin kudi da batun tsaro wanda gwamnan Kano Abdullahi Umar Ganduje yayi.

Emefiele yayin da yake amsa tambayoyin yan jarida yace baiga alakar batun sauyin kudi da kuma lamarin tsaron jihar Kano ba.

A baya bayannan dai gwamnan Kano ya bukaci shugaban kasa da ya dage ziyarar da ya shirya kawowa Kano, saboda batun tsaro dake da alaka da sauyin kudi da ake yi a ƙasar.

Emefiele yace baya son yayi musayar kalamai da gwamnan Kano Ganduje, domin yana ganinsa a matsayin dattijo, kuma wanda yake mutuntawa.

Daga bisani Emefiele yace zasu maida hankali kan aikin dake gabansu na sha’anin kudi a kasar nan.

Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a

Facebook. Alfijr Labarai
YouTube. Best Seller Channel
Twitter. @Musabestseller
Instagram. @musa_bestseller

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇

https://chat.whatsapp.com/Cy5n7eXK4wrHMIEYBSYpcQ

2 Replies to “Gwamnan Babban Bankin Najeriya Ya Mayarwa Da Ganduje Martani

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *