Na Tuba Na Bi Allah Na Kuma Daina Zage-Zage —Murja Kunya


Alfijr ta rawaito Murja Ibrahim Kunya, ta yi alkawarin daina zage-zage a shafukan sada zumunta na TikTok.

Hakan na zuwa ne bayan rundunar ƴan sandan jihar Kano ta cafke ta kan zargin yin zage-zage, batsa da kuma bata tarbiyya ta kafar sada zumunta.

Kunya wadda ake shirin gurfanarwa a gaban kotu, ta shaidawa ’yan sanda cewa, ta yi saukar Al-Kur’ani, kuma daga yanzu, “A bangaren zagi na yi alkawari na daina.”


Da take amsa tambayoyin Kakakin rundunar game da irin abubuwan da take yi a Soshiyal Midiya, wadanda al’umma ke tir da su, Murja ta ce, “Ai duk mai hankali ya san idan ya aikata ba daidai ba.”

Amma a kan zarginta da bata tarbiyya, cewa ta yi, “Da farko ni dai Murja ba waka nake yi ba balle in ce yara za su iya hawa wakata har tarbiyyarsu ta lalace.”

Game da zargin hawa wakokin batsa da makamantansu kuma, ta ce, “Gaskiya ni ba mace ba ce ma’abociyar yawan hawan wakokin batsa.”

Murja ta ƙara da cewa, ba ta taba sanin cewa wakar ‘Cas’ ta Ado Gwanja ta saba doka ba, shi ya sa ta hau wakar a Tiktok kuma ba ita ce farau ba.

Ta ci gaba da cewa ta fara cin karo da wakar Ado Gwanja ta ‘War’ ce a Soshiyal Midiya, kuma kafin ita dubban mutane sun hau wakar.

Wakojin biyu (Cas da War), sun tayar da kura, kan zargin yada badala, har Gwamnatin Tarayya ta hannun Hukumar NBC ta haramta sanya su a gidajen rediyo da talabijin.

A kan wakokin ne kuma wasu lauyoyi masu kishin jihar Kano suka maka Ado Gwanja a kotu kan zargin lalata tarbiyya.

“Maganar gaskiya game da zage-zage da na yi, zagi ne wanda na yi tun kafin a neme ni a wannan kotun da malamai suka shigar.

“Shi wannan zagi na farko abin da ya sa na yi shi akwai abin da ya faru wanda bidiyon wasu mata da ’ya’yansu da aka kama na gansu a wani daji, a lokacin mun yi roko don Allah don Annabi a taimaka a shiga lamarin wadannan mata da ’ya’ya a daji saboda iyaye ne.

“Shiru-shiru, sai abu ya kara rikicewa na ga an dauko bulala ana dukan wata mata da kananan yara a daji wanda hakan ya sa hankalina ya tashi na rika rusa ihu, na rasa abin da ke min dadi, na rasa ‘control’ dina na fito na rika wannan zage-zagen a kai.

“Zagi na biyu shi ne, wanda ya dauko hotona ya ce na rasu. Wannan ya sa aka kira ni a waya aka ce mini ai wani ya wallafa a soshiyal midiya, lokacin farkon fara Tiktok dina ne, ya wallafa cewa mun yi hatsari a hanyar dawowa ta daga Kaduna.

“An fada wa babarmu cewa mun yi hatsari na rasu, babarmu ta yanke jiki ta fadi na rasa ‘control’ dina shi ma na fito na yi zagi a kan wannan abun.

“Da na dawo gida sai da [aka] dauki awanni sosai wanda kowa ya san wannan, kafin mahaifiyata ta farfado.

“Daga wannan zagin guda biyu da na yi, tun daga lokacin da irin kalubalen da na fuskanta ka san a rayuwa wasu ba za su fahimci mene ne ya sa ka yi zagin ba, kai da ake gani laifinka za a gani.

“Na yi wa mahaifina alkawarin in Allah Ya yarda ba zan kara zagi a kan irin wadannan abubuwan ba.”

Game da sauran kalaman ta a Soshiyal Midiya da ke nuna rashin tarbiyya da batsa, mastahiyar ta ce ce: “Wakoki da ake magana a kaina, wakoki ne na Ado Isa Gwanja. Wanda na farko ya saki ‘War’, sai ta biyu ‘Cas’.

“Ita wannan War din da ya saki sama da mutum wajen dubu nawa sun hau, ina bibiya a Tiktok na hadu da ita ni ma na bi na hau wakar.

“Sai kuma ita Cas din, wanda mun yi waya da shi Ado Isa Gwanja ya ce na saki wakata.

Har ga Allah ban san wannan wakar tasa ta saba doka ba saboda yadda na ga mutane na amfani da wakar (a Tiktok) ya sa ni ma na hau wakar,” in ji Murja.

Game da matakin karatunta na addini da boko, Murja ta ce: “Na yi sauka a matakin karatun addini; Na Boko kuwa ban gama sakandare ba na daina.”

Ga ci gaba hirar tasu:

Kiyawa:  Kina ganin irin wadannan bidiyo da kike wanda akwai alamun rashin tarbiyya a cikinsu, kina ganin daidai ko ba daidai ba?

Murja: Gaskiya duk mutum mai hankali, akwai abin da idan kana yi kai da kanka ka san cewa ba daidai ba ne.

Amma duk mai bibiyar shafukana yana kallo ya san ina da ra’ayi irin na Allah ka kawo mana mafita a kan mu daina abubuwan da muke yi a soshiyal midiya.

Don ba na mantawa ko mako daya ba a yi ba sanadiyyar rasuwar da aka yi mana ta Kamal Aboki, na wallafa sako nake cewa Ya Ubangiji idan wata lalura ce za ta zama sanadiyyar shiryuwata ni Murja duba da yadda na ga Kamal ya rasu ana tare, Allah Ka dora mini wannan cutar.

Kiyawa: Ko kina nadamar abubuwan da kika yi wadanda suka shiga kafafen sada zumunta na zamani wanda za a iya cewa kusan har abada suna nan har ’ya’ya da jikokinki za su gani?

Murja: Abin da zan iya cewa shi ne, a bangaren zagi na yi alkawari na daina, da ma shi ne babban kalubale a rayuwa.

Kiyawa: Sauran bidiyo na yada batsa da makamantansu kuma fa?

Gaskiya ni ba mace ba ce ma’abociyar yawan hawan wakokin batsa.

Kiyawa: Yanzu za a ci gaba ke nan ko ya abin yake?

Murja: Tun kafin ma a kawo wannan martanin, tun a rasuwar da aka yi kamar yadda na fada a baya a kan mutuwar Kamal na ce, ko da wata lalurar ce za ta yi sanadiyyar shiyuwata Allah Ka nuna mini ita.

Kiyawa:

Aminiya.

Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a

Facebook.   Alfijr Labarai
YouTube.     Best Seller Channel
Twitter.        @Musabestseller
Instagram.  @musa_bestseller

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇

https://chat.whatsapp.com/Cy5n7eXK4wrHMIEYBSYpcQ

One Reply to “Na Tuba Na Bi Allah Na Kuma Daina Zage-Zage —Murja Kunya”

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *