Sarkin Kano Ya Bawa Shugaban Kasa Kyautar Ban Mamaki

Alfijr ta rawaito Mutane da dama sun cika da mamakin wai menene wannan Sarkin Kano ya damkawa Shugaba Muhammadu Buhari.

Kasancewar Sarkin Kano masanin Al’ada ne, shiyasa yayi masa kyautar Fulani, ta al’ada

A cikin kahon, Riga ce wadda ake kira BULLAM KO FARIN KANO,

RIga ta masu mulki, Riga ce wadda sai kasaitattun Sarakuna ke saka ta,
Riga ce wadda ba’a saka ta sai ranar Fita Kunya,

A jerin Rigunan Hausa, wannan Riga ta cikin kaho, tana daga Riguna mafi girman Daraja,

Don haka ne Mai martaba ya yiwa Shugaba Muhammadu Buhari kyautarta a matsayinsa na mutum mafi kololuwar daraja a kasa baki daya.

Wanda wannan daddiyar Al’ada ce tun bayan zuwan Fulani kasar Hausa.

Madallah da Samun Sarki masanin Al’ada, mai kuma Farfaɗo da al’ada.

Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a

Facebook. Alfijr Labarai
YouTube. Best Seller Channel
Twitter. @Musabestseller
Instagram. @musa_bestseller

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇

https://chat.whatsapp.com/Cy5n7eXK4wrHMIEYBSYpcQ

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *