Allah Ya Yiwa Tsohon Mataimakin Shugaban BUK Farfesa Ibrahim Umar Rasuwa


Alfijr ta rawaito Allah ya yiwa Farfesa Ibrahim Umar ya rasuwa a daren Litinin, sanarwar ta fito ne daga bakin ɗan sa, Farouk Ibrahim Umar ya tabbatar da babban rashin.

An gudanar da jana’izar marigayi fitaccen masanin kimiyyar lissafi a Kofar Kudu da safiyar Talata.

Marigayin, wanda ya yi aiki a matsayin VC na Jami ar Bayero Kano tsakanin 1979 zuwa 1986, shi ne shugaban cibiyar na uku.

Shi ne dan Najeriya na farko a fannin ilimin kimiyyar lissafi da ya fara koyarwa a jami’a a shekarar 1976.

Ya kasance memba a tawagar Najeriya a babban taron hukumar makamashin Nukiliya ta Duniya (IAEA) daga 1989.

kuma an nada shi Darakta-Janar na Hukumar Makamashi ta Najeriya 1989.

Ya taba zama shugaban hukumar IAEA a tsakanin 2000-2001 sannan a shekarar 2004 ya zama Darakta a Cibiyar bincike da horar da makamashi, inda aka fara samar da makamashin nukiliya na Najeriya.

Nadin nasa na karshe shine a shekarar 2007, lokacin yana cikin kwamitin bada shawarwari na kasa da kasa na taron karawa juna sani na kasa da kasa kan sabunta makamashi don ci gaba mai dorewa a Afirka, wanda aka gudanar a Jami’ar Nsukka a Najeriya.

Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a

Facebook. Alfijr Labarai
YouTube. Best Seller Channel
Twitter. @Musabestseller
Instagram. @musa_bestseller

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇

https://chat.whatsapp.com/Cy5n7eXK4wrHMIEYBSYpcQ

2 Replies to “Allah Ya Yiwa Tsohon Mataimakin Shugaban BUK Farfesa Ibrahim Umar Rasuwa

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *