Alfijr ta rawaito Hukumar shirya jarabawar shiga jami’a ta JAMB ta soke rajistar ɗalibai 817 a jarrabawar gama sakandare ta 2023 (UTME).
Magatakardar hukumar, Farfesa Ishaq Oloyede ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar a safiyar Laraba, 8 ga watan Fabrairu, 2023.
A cewar sanarwar, an yanke hukuncin ne sakamakon gano wasu laifuffuka kamar yin amfani da na’urar tantance kwayoyin halitta masu ban mamaki a lokacin rajistar.
Oloyede ya bayyana cewa, wasu jami’an rajista a cibiyoyin gwajin na’urar kwamfuta 178 da abin ya shafa sun kara da tambarin yatsu domin kammala rajistar ‘yan takarar.
Tsohon mataimakin shugaban jami’ar Ilorin, ya bayyana cewa daliban 817 da abin ya shafa za a sake ba su damar sake yin rijistar jarabawar tare da cibiyoyin da ke dauke da kudin.
Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a
Facebook. Alfijr Labarai
YouTube. Best Seller Channel
Twitter. @Musabestseller
Instagram. @musa_bestseller
Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇