Kotu Ta Daure Mai Binciken Kudi Kan Almundahanar N19m


Alfijr ta rawaito Babbar Kotun Jihar Yobe ta yanke wa Mai Binciken Kudi na Ma’ikatar Kananan Hukumomin Jihar hukuncin daurin shekara biyar a gidan gyaran hali da tarbiyya.

Alkalin kotun, Mai Shari’a Muhammad Lawu Lawan ne ya yanke hukuncin ranar Litinin, bayan  samun Alhaji Idris Yahaya da almundahanar Naira miliyan 19.

Hukumar Yaki da Cin Hanci da Rashawa ta kasa shiyyar Maiduguri, babban birnin Jihar Borno ne ya gurfanar da wanda ake zargin.

Kunshin tuhumar na cewar, ana zargin Alhaji Idris da karbi kudaden ne da nufin sayo wasu motoci kirar Toyota Corolla 2015, da za a yi amfani da su a ma’aikatar, amma ya karkatar da kudaden zuwa wata hanya ta daban.

An gurfanar da shi ne ranar Laraba, 9 ga watan Nuwamban 2022, in da aka yanke masa hukuncin bayan ya amsa aikata laifin da ake tuhumarsa dashi.

Da yake yanke hukuncin, Mai Shari’a Muhammad ya ce masu kara sun gabatar wa kotun gamsassun hujjojin da suka tabbatar da zargin da ake yi masa.

Daga nan ne ya yanke masa hukuncin daurin shekara biyar tare da zabin biyan tara.

A karshe mai shari’a ya umarci mai laifin ya biya Naira miliyan 10 da dubu 100 ga Gwamnatin Yobe ta hannun EFCC, koya shafe karin wasu shekaru biyu a daure.

Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a

Facebook.   Alfijr Labarai
YouTube.     Best Seller Channel
Twitter.        @Musabestseller
Instagram.  @musa_bestseller

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 

https://chat.whatsapp.com/G1wNveF9mGU7jec5mWhFvZ

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *