Gobara Ta Tashi A Kasuwar Biu Da Kasuwar
Gamboru Da Ke Maiduguri

Alfijr ta rawaito wasu munanan gobara na ci a kasuwar Gamboru da ke Maiduguri, babban birnin jihar.

Gobarar na zuwa ne a daidai lokacin da aka samu rahoton wata gobara a Babbar Kasuwar Biu da ke

jihar.

Gobara ta tashi ne a kasuwanin ana tsaka da zaben gwamnoni da ’yan majalisar dokokin jiha.

Mataimakin Shugaban Tsaro ta Sa- Kai ta CJTF, Aliyu Isa ya ce, sun samu sanarwar tashin gobarar ce da misalin karfe 9 na safiyar ranar Asabar.

Ya shaida cewa gobarar ta yi barna sosai a bangaren masu sayar da katako a kasuwar, amma jama’ar gari sun yi taron dangi wajen shawo kanta.

Amma ya cewa duk da haka, gobarar “Ta kawo tsaiko ga harkokin zabe a sassan garin, ko da yake daga baya jama’a sun koma sun ci gaba da zabe.

Kasuwar Gamboru ita ce kasuwa ta biyu mafi girma a Maiduguri, bayan Kasuwar Monday, wadda ta yi gobara, mako uku da suka gabata.

Aminiya

Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a

Facebook.   Alfijr Labarai
YouTube.     Best Seller Channel
Twitter.        @Musabestseller
Instagram.  @musa_bestseller

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 

https://chat.whatsapp.com/G1wNveF9mGU7jec5mWhFvZ

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *