A Tsawon Awa 24 Mun Ƙwato kuɗin Sata Kimanin Naira biliyan 4 A Najeriya – In Ji ICPC

ICPC Chairman

Dakta Musa Aliyu, shugaban hukumar yaki da laifukan cin hanci da rashawa da dangoginsu ta ICPC, ya ce cikin awanni 24, hukumar ta kwato Naira Biliyan 4 da jami’an gwamnati suka sace.

Alfijir Labarai ta rawaito Dakta Musa Aliyu, wanda babban lauya ne mai mukamin SAN, ya bayyana hakan ne a ranar Alhamis a Abuja a taron kwana guda na kungiyar yaki da cin hanci da rashawa ta NACC.

Ya ce hukumar ICPC za ta samar da matakai na fasahar zamani, mussaman fasahar AI wajen yaki da cin hanci da rashawa cikin sauki.

“A yau, ina son yabawa amfani da fasahar zamani wajen tabbatar da bin ka’ida wajen kashe kudi da shugabanci na gari.

” Fasahar zamani zata yi aiki cikin mamaki saboda baya nuna bangaranci kamar mutum. Zai taimaka mana wajen magance kalubale idan muka yi amfani da shi yadda yakamata.

“Wannan fasahar da nake fada, zata iya maganin abubuwa dayawa.

” Haka kuma, ina fada muku a wanni 24 da suka gabata, mun samu kwato Naira Biliyan 4 da aka sace aka tura asusun ajiya na kashin kai”, inji shi.

Acewarsa, abin damuwa ganin yadda ake karkatar da kudade.

Shugaban yayi kira ga majalisa da ta yi saurin amincewa da kudurin dokar kwarmata bayanai.

Domin samun sauran shirye shiryenmu zaku iya biyo mu ta wannan shafukan👇

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

https://www.threads.net/@alfijirlabarai

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇👇

https://chat.whatsapp.com/ELQRQyq1zGn7zpAVP8DwNj

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *