Alh Abba Khamis Bala Da ne ga Marigayi Alh Khamis Bala ya bayyanawa Alfijir Labarai wasu abubuwa dangane da rayuwar Mahaifin nasu.
Ya fara da cewar, ni ba Labari Aka ban ba dangane da rasuwarsa! A gabana ya rasu, yana kallo na ina kallon sa ido da ido.
Nunfashinsa ya fara kasa kasa lokaci guda! Na dade ina rokon Allah duk sanda zai dauki ransa ya kasasance bana wajan! Amman Allah bai kaddara hakan ba.
Ya kasance fiye da wata 3 yana jiyya a asibiti, amman babu ranar da ba tare muke kwana ba, ni da wasu daga cikin kannena sai gari ya waye sannan na koma gida nayi wanka sai kannena su ci gaba da kulawa kafin na dawo.
Yayin rasuwarsa ina kallon sa rai yana fita amman ba yanda muka iya, Alhamdulillah ya rasu cikin nutsuwa idanunsa biyu kuma a hankalinsa batare da yanajin jiki ba .
Kafin rasuwar tasa na zo gida yanda na saba sai ya saka aka kirani a waya muka yi maganganu, na ce masa gani nan zan dauko ruwan zafi na dawo, baifi awa 3 da dawowa ta ba ciwon ajali ya motsa, minti 5 zuwa 10 rai yayi halinsa ya koma ga Mahaliccinsa.
Abubuwan da ya kamata ayi koyi da shi a tsawon rayuwarsa sune!
Shi mutum ne mai Karɓar Kuskure
Shi Mutum ne mai zumuncin gaske.
Shi mutum ne mai Daraja Ɗan Adam.
Shi Mutan ne mai hakuri da Juriya
Shi mutum ne mai kaunar nasa.
Wani alkhairin nasama baya bari musani sai dai mugane.
A bangaren Karɓar kuskure komai kankantarka komai rashin darajarka idan kazo masa da magana ko gyara zai baka lokaci ku tattauna kuma ya karɓi abinda ka zo masa dashi cikin girmamawa.
Zumuncinsa ba wai kan yan uwa da yayansa yake ba, mutukar ya sanka zaka sha mamakin yadda zai dinga zumunci da kai, babban abinda baya so shine, rashin gaskiya amman indai ya fahimci kana da gaskiya baka da son zuciya nan take zai saki jiki dakai musamman MAKARANTA ALKUR’ANI wallahi a sani na kullum bayyi karatu sosai ba izu 18.
Darajar gidansu gidan makaranta ne to ko mahaukaci ne ya zo wajensa zaka ga yana bashi kulawa ta musamman, balle mai hankali.
Hakuri da juriyar yanayi ya saka shi da wuya kasan me yake ciki ko me yake damunsa, yakan kokarin komawa ga Allah domin shine mai warwarewa kowace irin larura bai taba kwanciya a asibiti ba sai wannan kwanciyar ta ajali .
Abu mafi burgewa da Marigayi Takawa shine idan dai ya sanka to babu shakka zaka ga kauna tare da shi a gareka ba wai sai yan uwansa ba ko yayansa, makota da yan unguwa da abokanan mu amula zasu shaida wannan.
Matsayin da Allah ya ajiye shi bai rudeshi ba, wajen jin wani abu a ransa.
A kullum na kan tuna yadda nake rayuwa da shi a matsayinsa na mahaifina kamar abokina ya maidani, ka ida ne Allah ke da kullum kafin sallar asuba ko bayan idarwa sai munyi waya, sannan idan na fito kafin tafiya wajan harkokina sai na shiga wajensa.
Sannan zamuyi waya 2 na rana da karfe 4 na yamma, idan kaga haka bata faru ba to muna tare da shi ne.
Akwai abinda bazan taba mantawa da shi ba nayi rashin lafiya shekara ɗaya zuwa 2 da ta wuce, amma bai sani ba saboda kar na daga masa hankali, yajini shiru ya kirani sai na yi masa karyar nayi tafiya ne sai kwana ya kama ni ba shiri, budar bakinsa sai yace ai da ka gayamin kafiin ka tafi sai na maka addu’a ai!
Nan take na bashi hakuri gami da jansa da hira kamar yadda muka saba.
Mahaifiya ta Hajiya ita ma ta kirani tace Abba tun jiya nake kiranka amma kaki zuwa!
Ban boye mata komai ba nace Hajiya ina kwance a asibiti ne kwana 2 yau shine dalili, na roke ta da karta gayawa Takawa saboda karya daga hankalinsa, tayi min addu’a muka yi sallama.
Karfe 9 na dare kawai sai gashi a kaina duk da dakin da nake a asibitin hawa na 2 ne, kuma shi gashi da matsalar kafa, shigowarsa ke da wuya sai ya hade rai, na lallaba na sakko daga gado na gaishe shi, sai ya ce min menene dalilin da baka da lafiya kake boyemin cewar baka gari?
Nace masa an kawo ni nan ne bana cikin hayyacina, a gaskiya idan ka ganni zaka shiga damuwa duk da baka da hawan jini balle Sugar ko wani ciwo na daban, sai ciwon kafa da kake fama da ita, da ƙyar muka lallaba da Auwal bayan asibitin sun turo mota muka tafi wajan 1 na dare, sanin cewar idan ka ganni a lokacin zaka fini shiga damuwa ne ya saka na boye maka, don Allah kayi hakuri.
Lokaci guda ya fahimceni ya kuma kama murmushi hadi da yimin kyawawan Addu’o’i.
Nayi kokarin rakashi su tafi yace a nan zai kwana, da yan da baru na lallabashi ya yadda suka tafi da mahmud, nayi karfin hali na tattako har zuwa wajen mota na rakosu cikin horewar Allah, kafin zuwansu bana iya ko takawar da kafar.
Washegari aka sallameni na dawo gida, sannan na tafi harkokina bai yi aune ba wajen sallar isha sai ya ganni a wajensa a masallacin Sarki, sai murna da farin cikin gani na nazauna muka yi ta hira daga karshe na taho gida.
Daga lokacin da ya kwanta ciwo zuwa rasuwarsa, idan zamu yi magana da shi, zai yi Umarnin kowa ya bamu waje.
Alhamdulillah sakamakon wannan ganawar da muke ina ganin a cikin kasi 💯 na abinda ya kamata nasani ko ya barmin Wasiyya ina ganin ya gayamin kaso 90% .
Alhamdulillahi a zamantakewarmu ko wani umarnin zai bada ko kuma yana son ayi masa, mafi yawan lokaci ni zai kira sabo da soyayya bana gidan ina gidana amman ni zai ce nagayawa wani agidan yayi masa . ganin nayi aure bai sa yajanye min wani aikin da nake masa ba kafin nayi aure a wajansa duk dayane kuma wallahi duk kauna ce , kuma nafi kowa kusanci da shi badan nafi sauran yan uwana a wajansa ba . ko magana akeso a gayamasa ni ake gayawa saboda fahimta da sanin yanda zan masa bayani batare da nuna damuwaba . akwai kunya da jin nauyi tsakaninmu! Nasan abinda yake so haka abinda baya so ko da ido ya kalleni nasan manufarsa.
Yakan gayamin cewar ABBA ina yi wa kowa Addu’a amman taka Ta dabance.
Kafin rasuwarsa muna cikin ICU da kansa yake min ishara da cewar bazai tashiba yana gani lokaci yayi.
Ya gayamin cewar yayi mafarki da ƙaninsa Baba SADI yana cewa yanzu ALH HAMISU tafiya zakai kabarni! saboda wannan mafarkin ya nuna masa wasu alamu wanda ke masa nuni da zai tafi yabar yan uwansa ma ana qa Ida takusa cika
Shine da kansa yake gayamin wannan mafarkin nasa kafin komawarsa ga mahaliccinsa
Munyi rashin mutumin kirki mahaifi abin alfahari, har yanzu ban daina kukan rashinsa ba sai dai dauriya da karbar abinda Allah ya kawo.
Ina kara neman addu arku a gareshi yan uwa masu albarka.
Allah ya gafarta masa halinsa na gari ya bishi yau 29 ga Afrilu 2023 kwanansa 40 da rasuwa
Wannan wasu kadan daga cikin halayen mahaifinmu kenan.


Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a
https://twitter.com/Musabestseller?s=09
https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165
https://www.threads.net/@alfijirlabarai
https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12
https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag
Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijir Labarai 👇
https://chat.whatsapp.com/CJ2q8cmhhOxFY6OEgwV5vk