
Alfijr ta rawaito yau shekara 25 da rasuwar tsohon shugaban kasar Najeriya na mulki Soja, Janar Sani Abacha.
A ranar 8 ga watan Juni 1998 janar Sani Abacha ya rasu.
Rasuwarsa tasa ta girgiza jama’a musamman ganin cewa bai kwanta jinya ba, lokaci daya kwatsam.
Marigayin ya rasu ne a jajibirin ranar da ya gudanar da ayyukansa kamar yada ya saba a matsayinsa na kwamandan askarawan Najeriya.
Uwargidan marigayin Haj Maryam Abacha ta ce iyalinsa na yi wa marigayin adu’o’i a duk ranar zagayowar mutuwarsa.
“Muna adu’o’i da mu da mutanen gida da limamanmu na gida, mu na fida’u, mu na mi shi adu’o’i” a cewarta.
A cewarta marigayin mutum ne mai son yin raha da iyalinsa da kuma motsa jiki.
“Zai tashi da safe ya yi adu’a irinta adininsa, ya shirya ya tafi wurin aiki kuma ya dawo ya ci gaba da harkokinsa”, in ji ta.
Rayauwar marigayi Sani Abacha
A ranar 20 ga watan Satumba ta shekarar 1944 aka haifi Sani Abacha a Kano.
Ya yi makarantar Firamari ta City Senior Primary School, Kano, Government College, Kano, 1957-1962.
Ya halarci Kwalejin horas da sojoji ta Kaduna Najeriya daga 1962-1963.
Sannan ya wuce kwalejin Horas da Sojoji ta Aldershot da ke Ingila a 1963, Kwalejin horas da dakarun kasa ta Warminster ta Birtaniya 1966.
A 1971 a halarci kwalejin sojoji ta Jaji da ke Kaduna Najeriya zuwa1976.
Sannan ya yi kwalejin nazarin manufofi da tsara dabarun mulki ta Kuru, Jos a 1981.
Ya yi kuma wasu kwasa-kwasai da suka shafi harkar tsaro a Canada, Amurka a shekarar 1982.
Tun daga juyin mulki na farko a Najeriya a shekarar 1966 janar Sani Abacha ke taka rawar gani sai wanda aka yiwa Shagari da na Babangida da kuma wanda yaiwa Cif Ernest Shenakon.
Tsawon shekarun da ya yi kan mulki Abacha ya yi mulki a matsayin shugaban kasa kuma babban kwamadan sojojin tarayyar Najeriya daga 1993 zuwa 1998.
Rawar da ya taka a tattalin arzikin Najeriya
A karkashin mulkinsa ne asusun kuɗaɗen wajen kasar ya karu daga dala miliyan 494 a 1993 zuwa dala biliyan 9.6 a tsakiyar 1997 sannan ta rage bashin da ake bin kasar daga dala biliyan 36 a 1993 zuwa dala biliyan 27 a 1997.
Mutuwarsa
A ranar 8 ga watan Yunin 1998, janarar Abacha ya rasu a fadar shugaban kasa.
Gwamnatin kasar ta bayyana bugun zuciya a matsayin abinda ya yi sanadin mutuwarsa, sai dai jami’an diflomasiya na kasashen waje, ciki har da manazarta leken asirin Amurka, sun ce mai yiwuwa an sanya masa guba ne.
Ga wasu ‘yan Najeriya marigayi Abacha shugaban kasa ne da ya taka rawar gani wajan kawo ci gaba ga kasar, yayin da wasu kuwa na kallonsa a matsayin shugaba mai mulki kama karya.
Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a
Facebook. Alfijr Labarai
YouTube. Best Seller Channel
Twitter. @Musabestseller
Instagram. @musa_bestseller
Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇
https://chat.whatsapp.com/GdLiqZyHuSz5NhjdGoGRGZ