Akwai Ƴan Nijeriyan Da Sun Fi Ni Karfin Kudi – Dangote

Screenshot 20240722 150031 Facebook

Daga Aminu Bala Madobi

Attajirin da ya fi kowa kudi a Afirka, Aliko Dangote, ya ce akwai ƴan Najeriyan da su ka fi shi karfin kudi idan aka kwatanta da shi.

Alfijir labarai ta ruwaito da yake jawabi ga ’yan majalisar wakilai da suka ziyarci matatar man sa a Legas a ranar Asabar, hamshakin attajirin ya ce ba a yi masa adalci ba da ake cewa ya kankane komai a harkar kasuwanci a Nijeriya.

Dangote ya ce suffanta kamfanin sa a matsayin wanda ya kankane kasuwanci abin takaici ne, inda ya kara da cewa hakan ya sa ya fasa saka hannun jari a harkar karafa.

“Kankane kasuwanci shine hana mutane da kuma toshe musu hanyar kasuwanci na halal. A’a, wani bigire ne da kowa ya ke da dama kamar misali, abinda za a baiwa kamfanin siminti na Dangote, haka wasu za su samu sama da namu kason ma,” inji shi.

Sai dai ya karfafa gwiwar ‘yan Najeriya da su sanya hannun jari a masana’antar don taimakawa wajen bunkasa tattalin arzikin kasar.

“ina ƙarfafa wa sauran ‘yan Najeriya gwiwa da su je su yi. Ba mu kadai ba ne a nan. Akwai ‘yan Najeriya da suka fi mu kudi.

“Ya kamata mutane su kawo wannan kudin daga Dubai da sauran sassan duniya su zuba jari a kasarmu ta gado,” in ji Dangote.

Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

https://www.threads.net/@alfijirlabarai

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇👇

https://chat.whatsapp.com/ELQRQyq1zGn7zpAVP8DwNj

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *