Al’ajabi: Bafaranshe Yayi Tattaki Har Ƙasar Ivory Coast Dan Nemo Wadda Ta Raine Shi Tsawon Shekaru 38.

Daga

Aminu Bala Madobi

Alfijr ta rawaito wani Bafaranshe ya yi tattaki daga kasar Faransa zuwa kasar Ivory Coast dake nahiyar yammacin Afirka don neman wata tsohuwar mata da take yi renon shi a lokacin yana jariri.

Mai renon nasa wadda a yanzu tsufa yazo ma ta, ta kasance tana kula dashi shekaru 38 da suka gabata lokacin da yake zaune a kasar Ivory Coast tare da mahaifinsa.

Cikin wani tsohon ajiyayyen hoto ya nuna yadda matar ke ɗauke da Bafaranshen a bayanta lokacin yana jariri.

Rahotanni sun nuna cewa bayan cikar wa’adin aikin mahaifin bafaranshen, Mahaifinsa ya yi ritaya hakan yasa iyalan nasu suka yi kaura suka bar kasar Ivory Coast, hakan yasa suka dauki tsawon lokaci batareda ganawa ba da mai renon nasa.

Shekaru 38 bayan haka, yaron wanda yanzu ya zama mutum, ya koma kasar ta Ivory Coast don nemo matar da ta yi masa reno.

Majiyar Jaridar Alfijr ta rawaito cewa neman nasa ya yi nasara kuma ya yi farin ciki sosai lokacin da suka sake haduwa da juna. Sun dauki hoton junan su don tattara bayanan haduwar su.

Rahotanni sun ce, Bafaranshen ya bai wa tsohuwar wasu kudi kuma ya sanya mata alawus na wata-wata da zai dinga biyanta wasu kudade.

Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a

Facebook. Best seller Channel
YouTube. Best Seller Channel
Twitter. @Musabestseller
Instagram. @musa_bestseller

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇

https://chat.whatsapp.com/I4L1E0rIZp23nVG7Mtt47c

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *