Amarya Rarara Aisha Humaira ta magantu akan masu yi mata ƙage da sharri da ƙazafi

FB IMG 1745604806040

Aisha Humaira, amaryar kuma abokiyar aikin mawaki Dauda Kahutu Rarara ta magantu a karon farko bayan auren su, wanda aka daura a Maiduguri a ranar Juma’a.

A wani faifen bidiyo da ya karade kafafen sadarwa, an gano Aisha Humaira sanye da hijabi tana kira ga waɗanda ke fadar maganganu na ƙage akan alaƙar ta da Rarara da su dena kuma ta yafe musu.

“Ina masharranta, ina munafukai, ina masu shedar zir, ko kuma wani ya ji labari ha je ya dorar? Ina masu zama su ce wance ta yi kaza, wane ya yi kaza, an yi kaza, an yi kaza kuma bayan duk basu gani ba ba su ji ba.

“Ina wadanda su ka zage ni ban sani ba, ina waɗanda su ka zage ni na sani? Ina magulmata masu kaiwa da kawowa, masu cewa Aisha Humaira ta yi kaza, ta yi kaza?

“Duk wanda ya zage ni a bayan ido na da wanda ya zage ni d gaban wani, ka je kana cewa Humaira ta yi kaza alhalin watakila ba ka san ni ba?

“To ina me muku albishir cewa wallahi dukkan ku ma na yafe muku. Allah Ya yafe mana kurakuran mu Ya shiryar da mu shiri na addinin Musulunci.

“Wallahi na yafe wa kowa da ya zage Ni ko ya fadi wani abu da bai sani ba a kaina ko ya min ƙazafi alfarmar Annabi Muhammadu Sallallahu alaihi Wasallama. Na yafe muku duniya da lahira. Allah Ya yafe mana baki daya, Ya saka mu a aljanna baki ɗaya,” in ji Humaira, a bidiyo mai tsawon minti 1:12.

Daily Nigerian

Domin samun sauran shirye-shiryen Alfijir labarai/Alfijir news ku shiga nan  👇

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

https://www.threads.net/@alfijirlabarai

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

Alfijir labarai Alfijir News Whatsapp Group 👇👇

https://chat.whatsapp.com/KoLt2IMlnQfJPP6zNrcNKD

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *