Lauyoyin Murja Kunya sun zare hannunsu daga kare ta bayan ta karya umarnin kotu
Alfijir labarai ta ruwaito Lauyoyin Murja Ibrahim Kunya sun ce sun yi nadamar tsaya mata, bayan da ta ci gaba fitar da bidiyo a TikTok duk da umarnin Kotu na hana ta yin hakan.
Sun ce nan gaba kaɗan za su bayyana matsayarsu a kan shari’ar da ake da ita.
Sai dai a tattaunawar Murja tayi da DCL ta ce, nayi bankwana da jihar Kano har abada, domin babu abinda nake nema a cikinta yanzu.
Ta kara da cewar an yaudareni akan shari’ar, an cemin idan 16 ga watan nan tayi zan iya cigaba da posting na kuma jinkirta sai 17 sannan na fara , amma anzo Ana min surutai! Kun bani kunya wallahi.
Don haka na bar garin duk ne naima na ya zo inda nake
Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a
https://twitter.com/Musabestseller?s=09
https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165
https://www.threads.net/@alfijirlabarai
https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12
https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag
Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇👇
https://chat.whatsapp.com/IUuk7jeH4yvAkwOmbOCSfl